Masu dauke da cutar Coronavirus a nahiyar Afrika sun nunka a cikin mako daya. Wani rahoto da Wprldometer ta fito da shi a yau Lahadi da safe, ya nuna cewa wadanda suka kamu a Afrika daga ranar Litinin da ta gabata zuwa yau Lahadi, sun nunka wadanda suka fara kamuwa tun bayan farkon bullar cutar.
Rahoton ya tabbatar da cewa yanzu akwai mutane sama da 4,000 da suka kamu a Afrika.
A ranar 4 Ga Maris ne aka fara samun mutum na farko da cutar ta kama a Afrika ta Kudu. Ya zuwa makon da ya gabata, an samu adadin mutum 554. Amma kuma a jiya Asabar, na samu mutum sama da 1000 a Afrika ta Kudu.
“Mutum sama da 4000 suka kamu a Afrika. An samu rahotannin mutuwar mutum 131, kuma wasu 236 an rigaya ma an sallame su.” Haka rahoto ya tabbatar da cewa kasashe 46 daga cikin 54 na fadin Nahiyar Afrika duk cutar ta bulla a cikin su.
Sai dai kuma Worldometer ta ce har yanzu yawan masu dauke da cutar a Afrika ko kadan ba su kai yawan wadanda suka kamu ko ba a Turai, Asiya da Amurka ta Arewa.
Akwai kasashe takwai na Afrika da har yau Coronavirus ba ta bulla a can ba. Sun hada da:_Botswana, Burundi, Comoras, Malawi, Sao Time & Principe, Sierra Leone da Sudan ta Kudu.
Kasashen da ta fi yi wa illa sun hada Afrika ta Kudu mai sama da mutum 1,000. Sai kuma Masar da Aljeriya da Morocco kowace ta kama sama da mutum 400.
Kasashen Tunisiya, Burkina Fasso kuwa kowace sama da mutum 200 ya kamu.
A Najeriya an kai ga mutum 111, yayin da akwai wasu kasashen da sama da mutum 100 suka kamu, sai kuma masu kasa da mutum 50 kowace.