CORONAVIRUS: Mutum 14 sun kamu a Najeriya, yanzu 111

0

Hukumar NCDC ta bayyana cewa an samu Karin mutane 14 da suka kamu da cutar coronavirus a Najeriya a ranar Lahadi.

Mutum 9 a Legas, 5 a Abuja.

Yanzu akalla mutum 111 kenan suka kamu a Najeriya.

Jihar Legas na da mutum 68 da suka kamu da cutar zuwa yanzu, Abuja 21, Ogun 3, Oyo 7, Enugu, Edo da Bauchi, bibbiyu, Ekiti, Benuwai daya, Osun 2, Ribas 1,
Kaduna 1.

Za a iya samun Karin yawan mutanen da suka kamu da cutar a kasar nan ganin yadda gwamnati ta maida hankali wajen gano wadanda suka yi cudanya da wadanda suka kamu.

A jawabin da shugaban Kasa Muhammadu Buhari yayi wa ‘yan Najeriya ranar lahadi ya ce gwamnati ta saka dokar garkame garin Abuja da Legas na makonni biyu har sai an kammala yin gwajin wadanda ake zargin sun kamu da cutar.

Attajirai da manyan bankunan Najeriya suna ta aikawa da gudunmawarsu ga hukumar NCDC, domin tallafa mata wajen aikin kau da cutar da take yi.

Hatta ministocin Najeriya sun bada gudunmawar rabin albashin su na watan Maris ga wannan hukumar.

A duniya kuma mutane sama da 600,000 aka tabbatar sun kamu sannan akalla 27,000 sun mutu.

Kasar Spain da Italiya ke kan gaba wajen yawan mutanen da ke mutuwa a kullum a dalilin kamuwa da cutar.

Sama da Mutane 500 suke mutuwa a kullum daga wadannan kasashe.

Ita ma kasar Amurka ta bi sawun kasashen da cutar ta dabaibaye.

Yanzu ta fi kowacce kasa a duniya yawan wadanda suka kamu da cutar, sannan akwai sama da mutum 1000 da suka kamu.

A Nahiyar Afrika, har yanzu akwai kasashen da basu kamu da cutar ba. Sai dai kasashe kamar su Afrika ta Kudu da wasu manyan kasashen nahiyar sun fada tsundum ciki.

Kasashen Bostwana, Burundi, Lesotho, Malawi, da wasu tsiraru basu samu bayyanan cutar a kasashen su ba. Sai dai sun dauki matakan kare mutanen su.

Share.

game da Author