Gwamnatin Kano ta kama Almajirai 1500, ta maida su jihohin su

0

Idan ba a manta ba, gwamnatin jihar Kano ta bayyana dokar hana bara a fadn jihar makonni biyu da suka wuce.

Duk da cewa wannan shiri ya samu suka daga mutane da dama suna kokawa cewa bai dace a hana almajirci kai tsaye ba, gwamnatin ta toshe kunnen ta.

A ranar Juma’a Hukumar Hibzah karkashin shugabancin Lawan Fagge, ta sanar cewa ta kama Almajirai 1500 suna gararamba a fadin jihar kuma wadanda aka kama duk ‘yan shekara 7 ne zuwa 15.

Sannan kuma ya ce akwai wasu da tsuffin mata ne dake bara haka kawai don jin dadi duk da ‘yan uwansu sun hanasu.

” A cikin wadanda muka kama kuma muka maida su jihohin su, jihar Katsina ce ta fi yawan Almajiran. Daga ita sai jihohin Zamfara, Kebbi, Borno, Yobe, Kano da Adamawa.”

Fagge ya ce tuni an maida wadannan yara jihohin su domin a danka wa Iyayen su. Ya ce akwai wasanda tundaga kasar Nijar da Chadi ma suka shiga jihar yin Almajirci.

Baya ga yara da aka kama akwai tsuffin mata da aka ma suma da ke bara a titunan jihar. Suma duk an maida su ga ‘yan uwan su.

Sai dai Fagge ya ce tun kafin a fara kamen wasu iyayen sun zo sun dauke ‘yayan su tun da wuri kafin ya kai ga mun ma damke su.

A karshe gwamnati ta ce wannan doka na nan daram a jihar saboda haka kowa ya shiga taitayin sa.

Share.

game da Author