ZABEN AKWA IBOM: An yi ‘garkuwa’ da jami’an zabe a mazabar Minista Akpabio -INEC

0

An tsare wasu jami’an Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC a makarantar sakandare ta Esseien Udim, a Akwa Ibom, a daidai lokacin da ake ci gaba da kada kuri’ar zabukan cike gurabu da wadanda ba su kammalu ba a ranar Asabar a kasar nan.

PREMIUM TIMES ta tabbatar da cewa sakandaren mai suna Independent High School, ta na garin Ukana, a inda nan ne rumfar zabe ta PU9, a Ukana ta Yamma, inda can ne mazabar Ministan Jarkokin Neja Delta, Godswill Akpabio ta ke.

“An tare jami’an zabe a sakandaren Independent ta Ukana. Sun ji labarin cewa wasu mutane sun yi shigar basaja, a matsayin su DSS ne ko sojoji. Za ta iya yiwuwa kuma duk na gaske ne.

“An kuma shaida mana cewa an kwace wayoyin su, shi ya sa mu ka kasa samun su domin sanin halin da suke ciki.

Sahihiyar majiya ta ce mana wadanda suka je a matsayin jami’an tsaro, sun dauke gindi ‘yan daba da ‘yan jagaliya sun hana a yi amfani da na’urar zabe, ana ta dangwale kuri’u babu kakkautawa.”

Haka wani jami’i ya shaida wajen karfe 12:30 na rana.

Sannan kuma ya ce an kwace kayan zabe tun karfe 6 na safe.

“Duk da irin kokarin da mu ka yi na ganin mun yi komai a kan tsarin doka, komai ya tafi daidai, amma sai da wasu suka tarwatsa harkar zabe a karamar hukuma daya,” inji jami’in INEC.

Har zuwa karfe 1:52 na rana dai Kakakin INEC a Akwa Ibom, ya ce jami’an zaben na can a tsare ba a sake su ba.

Dama kuma da farko sai da jami’an SARS suka hana ‘yan jarida shiga wannan mazaba ta cikin wannan sakandare, har sai da kakakin ‘yan sandan jihar Akwa Ibom ya sa baki tukunna.

Idan za a tuna dai, Sanata Akpabio ya ce ya fasa shiga zaben na wannan karamar hukuma, ganin cewa da wahalar gaske ya yi nasara, kuma ya rigaya ya samu mukamin Minista na Harkokin Neja Delta.

Share.

game da Author