Rundunar ’Yan Sanda ta Abuja, FCT ta yi awon gaba da Sarkin Bwari, Muhammad Baba, bayan da wasu hasalallu suka kashe wani jami’in ‘yan sanda mai mukamin ASP a fadar sa.
Kakakin Yada Labarai na ‘Yan Sandan Abuja, Anjuguri Mamzah ne ya bayyana haka a cikin wata takarda da ya raba wa manema labarai.
Ya ce an kuma kama sakataren fadar sarkin mai suna Danlami Busa.
Manzah ya ce an yi wa ASP Eric Isaiah kisan-gilla a Fadar Sarkin Bwari, a lokacin da ya je ya ke kokarin kama wani mai suna Moses Peter, wanda aka fi sani da lakabin Dogo.
Jami’an tsaro dai sun yi kokarin kama Dogo ne, bayan zargin sa da aka yi da laifin kisan kai.
Anjuguri ya ce wani mai suna Dominic Emmanuel ne ya kai kara a ranar 21 Ga Janairu a Ofishin ’Yan Sanda na Bwari, ya ce an tsinci dan uwan sa Moses kwance rai-kwakwai-mutu-kwakwai, bayan an ji masa mummnan rauni.
Kakakin Yada Labarai har ila yau ya kara da cewa an garzaya da Moses asibitin Bwari, kamar yadda dan uwan sa ya yi wa ’yan sanda bayani.
A can ne Moses ya takarkare ya bada bayanin abin da ya faru da shi, inda bayan ya gama bayani sai ya mutu.
Ya ce an zargi Dogo shi da wani mai suna John da laifin kashe Moses.
Daga nan ne sai DPO na Bwari ya tura jami’an sa domin su je garin Ushafa su binciko yadda al’amarin ya faru.
“Sun je garin kuma suka yi arba da Moses, wato Dogo, amma ya ki mika kai a hannun ‘yan sanda. Maimakon haka, sai ya yi kururuwar kirawo abokan sa domin su kai masa dauki.
“Abokan wanda ake zargi, wato Moses Dogo, sai suka ce ba su yarda ’yan sanda su tafi da shi ba, sai an fara zuwa fadar Sarkin Ushafa tukunna.
“Daga nan sai jami’an ’yan sandan su biyu suka bi dandazon matasa aka tafi fadar sarki, inda suka samu sakataren sarki a fadar.
“Maimakon sakataren ya sa baki, sai ya tunzira dandazon jama’a, su kuma suka hau kan ’yan sandan da duka.
“Daga nan sai aka yi sauri aka tura jami’an tsaro a karkashin ASP Eric Isaiah tare da wasu ’yan sanda uku domin su kai wa wadancan biyun daukin gaggawa.
“Sun isa wurin da mota kirar Hilux, wadda aka yi amfani da ita aka kubuto wadancan ’yan sanda biyu, tare da Dogo, wanda suka yi nasarar arcewa da shi a hannun su.
“Abin bakin ciki, sai hasalallun matasa suka rufe su da duka, har suka kashe ASP Eric Isaiah. Sannan kuma suka ji wa sauran ’yan sanda raunuka.”
Kwamishinan ’Yan Sanda na Abuja, FCT, Bala Ciroma ya yi tir da kisan da aka yi wa ASP Isaiah.
Ya kuma bada umarnin sai an kamo wadanda suka kashe dan sandan an hukunta su.