Najeriya za ta ciwo bashin dala biliyan 1 don inganta harkar noma – Minista Nanono

0

Ministan Harkokin Noma da Raya Karkara, Sabo Nanono, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya za ta ciwo bashin dala biliyan 1 domin sawo kayan noma na zamani ta raba wa manoma.

Nanono ya yi wannan bayanin ranar Juma’a a Abuja a lokacin da ya ke kaddamar da kwamitin Shirin Inganta Noma na Green Imperative Programme.

Ya ce za a karbo bashin daga Deutsche Bank na Jamus, Brazilian Development Bank da kuma Bankin Musulunci, wato Islamic Development Bank.

Ministan ya ce an kulla yarjejeniyar biyan bashin nan da zuwa shekaru 15.

Kuma kashi 3 bisa 100 kadai za a biya kudin ruwa.

Idan ba a manta ba, Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ya kaddamar da Shirin Karin Wadata Abinci na Duniya, wato More Food International cikin watan Janairu, 2019, wanda shiri nre da Brazil ta fara kirkirowa domin tallafa wa wajen inganta noma a fadin duniya.

Wannan shiri idan aka karbo bashin dai kamar yadda Nanono ya bayyana, za a sayo kayan aikin noma ne domin a raba wa manoma a fadin kananan hukumomi 774 na fadin kasar nan.

“Idan wadannan kudade suka zo hannu, Najeriya za ta sayo taraktocin noma 10,000 sai sauran kayan aikin noma daban-daban har guda 50,000 da za a yi aikin hada su a nan Najeriya.”

Sauran abin da za a yi da kudaden kuwa, kamar yadda Nanono ya bayyana, sun hada da bayar da horo ga manoma rukuni daban-daban har tsawon shekaru 10, da kuma kakkafa cibiyoyin harkokin noma a kananan hukumomi a wurare 780 a kasar nan.

Minista ya ce taraktocin noma a kasar Kenya sun wadaci manoma, ba kamar nan Najeriya ba, inda suke da karanci sosai.
Ya ce idan aka sayo taraktocin, zai kasance.

Wannan bashi da za a ciwo dai ya nuna Najeriya ba ta saduda daga karbo bashi ba. Buhari ya ciwo bashi mai tarin yawa a tsawon lokacin da ya shafe na shekaru hudu a kan mulki ko ma a ce biyar.

Buhari ya samu ana bin Najeriya bashin dala biliyan 10.32 cikin 20185. Amma yanzu bashin da ake bin Najeriya ya kai naira tiriliyan 24.947, kwatankwacin dala bilyan 81.274.

Sannan kusan kashi 50 bisa 100 na kudaden shigar kasar nan, a biyan bashi ya ke tafiya kowane wata.

Nanono shi ne ministan da ya ce dan Najeriya zai iya rayuwa a kan abincin naira 30, kuma har ya ci ya koshi.

Ya yi ikirarin cewa ya san inda talaka ke take cikin sa da abincin naira 30 a Kano.

Share.

game da Author