Najeriya za ta fara rige-rigen tafiya duniyar wata – Ministan Fasaha

0

Ministan Kimiyya, Fasaha da Kirkire-kirkire, Ogbonnaya Onu, ya bayyana muhimmancin ilmin kimiyya da fasaha, inda ya kara da cewa nan ba da dadewa ba Najeriya za ta fara rige-rigen tafiya duniyar wata, tsakanin da sauran kasashen da ke zuwa bincike a sararin samaniya.

Daga nan ya kara da cewa karfin tattalin arzikin kowace kara ya dorane ga irin gagarimin ci gaban da kasar ta samu a fannonin kimiyya da fasaha.

Onu ya yi wannan jawabi ne a taron Tsoffin Daliban Izzi, wanda ya gudana a Tsangayar Ilmi ta Jami’ar Ebonyi da ke Ishieke.

Ministan ya ce gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta karfafa fannin kimiyya da fasaha a kasar nan, domin ya kasance jagora wajen fafada hanyoyin inganta tattalin arziki.

Daga nan sai ya yi kira ga malamai da su kara wa dalibai kwarain guiwa ta hanyar ba su shawarwarin nakaltar nazarin da kwasa-kwasan kimiyya, fasala da injiniya.

“Bayan rera taken Najeriya, an tambayi dalibai wane kwas kowa ke so a rayuwar sa, amma babu wanda ya ambaci injiniya.

“Abin bakin ciki ne idan a wannan makarantar a yanzu babu wanda ke da muradin zama injiniya.

“Saboda yanzu haka a Najeriya mu na nan mu na shirin fara cilla masu bincike zuwa duniyar wata.

“Kada ma ku yi tunanin hakan ba mai yiwuwa ba ne. Watakila a dauki shekaru 20 zuwa 30 nan gaba, amma dai mu na da wannan tsarin rubuce a kasa.

“Zan yi farin cikin ganin an cilla wani dan wannan makarantar wata rana a duniyar wata, domin yay i bincike. Hakan kuwa ba mai yiwuwa ba ne, har sai an yi karatun injiniya.”

Idan ba a manta ba, farkon nada ministocin Buhari ne a Minista Onu ya ce nan ba da dadewa ba Najeriya za ta fara kera fensir.

Share.

game da Author