HARAJI: Sai 1 ga Fabrairu za a fara cirar harajin jiki-magayi – Minista Zainab

0

Ministar Harkokin Kudade, Kasafi da tsare-tsare, Zainab Ahmed, ta bayyana cewa Akanta Janar na Kasa, Ahmed Idris ya kwafsa da ya ce an fara karbar haraji tun daga ranar Litinin da ta gabata.

Jiya ne Idris ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta fara karbar harajin na karin 7.5 bisa 100 tun daga ranar Talata, 13 Ga Janairu.

A ranar Litinin ce Shugaba Muhammadu Buhari ya sa wa dokar Karin Harajin Jiki-magayi hannu, inda VAT ya tashi daga kashi 5 bisa 100 ya koma kahi 7.5 bisa 100.

Kwatsam, jiya Alhamis sai Akanta Janar ya kira taron manema labarai, inda ya bayyana cewa daga ranar Litinin ce za fara karbar harajin jiki-magayi, wato VAT, wanda Gwamnatin Muhammadu Buhari ta kara daga kashi 5 zuwa kashi 7.5 daga wasu kayyayakin da ’yan Najeriya ke saye, sayarwa ko wasu huldodin kasuwancin da suka yi.

Babban Akawun Najeriya, Ahmed Idris ne ya bayyana ranar fara karbar harajin, kasancewa Shugaba Muhammadu Buhari ya saw a Dokar Kara Haraji Hannu a ranar Litinin da gabata.

Yayin da ya ke tattaunawa da manema labarai a ofishin sa, Idris ya yinkarin hasken cewa wannan sabuwar doka duk wasu kudaden da gwamnatin tarayya ta biya daga asusun ta, to za a fara cire kashi 7.5 na haraji nan take.

“A tsarin gwamnati, ba za ka fara aiwatar da wani tsari ba, har sai an samar da dokar da ta bada umarnin yin haka tukunna.

“ Ranar Litinin da ta gabata Shugaban Kasa ya sa wa Dokar Karin Haraji hannu, daga kashi 5 zuwa 7.5. washegari Talata sai aka kawo min lissafin biyan wasu kudi na watan Disamba, amma sai na ga an cire kashi 5 bisa 100 na haraji kadai. Ni kuma na ce ba zai yiwu ba.

“Na ce musu su je su buga sabon lissafi, su cire kashi 7.5 bisa 100 ba kashi 5 na tsohuwar doka ka.

“ Ita doka daga ranar da aka kafa ta, to ko da tsohon aikin da ka yi za a biya ka kudi, ka yi aikin ne kafin dokar, muddin za a biya ka bayan an kafa dokar, to da sabon lissafin doka za a biya ka.”

To amma da ta ke jawabi wajen rantsar da mambobin Gudanarwar Hukumar Tara Kudaden Shiga ta Kasa (FIRS), a jiya Alhamis a Abuja, Zainab ta ce sai ranar 1 Ga Fabrairu sannan dokar karin kudin harajin za ta fara aiki tukunna.

Daga nan ta yi kira ga mambobin hukumar gudanarwar FIRS su jajirce wajen tabbatar da cewa hukumar ta cimma kudirin da aka dauka za ta cimma, wato na tattara makudan kudaden harajin da ba na kudaden ribar man fetur ba.

Shi ma Shugaban FIRS, Muhammad Nami, ya yi kira ga mambobin su hada kai domin a cimma nasarar da aka tunkara a yanzu.

Share.

game da Author