JIGAWA: An haramta tadin dare tsakanin mace da namiji a karamar hukumar Kirikasamma

0

A dalilin fitsara da mata da maza suke yi a wajen tadi da suke yi da dare a Karamar hukumar Kirikasamma dake jihar Jigawa, karamar hukumar ta haramta duk wani haduwa na mace da namiji da dare a wannan karamar hukuma.

Babban dalili kuwa shine yadda ake samun mata da yaya na daukar ciki a wajen wannan tadi da akan kebe tsakanin namiji da mace.

Iyaye da dama sun rika kawo karar cewa ana yi wa ya’yan su mata ciki a wajen tadin dare da samarin su ke garzayowa. Sun roki hukuma su yi wani abu akai.

Jami’in hulda da jama’a na karamar hukumar Sanusi Doro, ya bayyana cewa tuni shugaban karamar hukumar Salisu Kubayo ya saka wa wannan doka hannu.

Duk wanda aka kama ya kebe da wata yarinya da daddare da sunan suna tadi, za a ci shi tarar naira 50,000 ko kuma zaman gidan Kaso na wata shida.

Dokar ta ce daga yanzu kowa zai ga budurwarsa zai yi haka ne da rana tsaka.

Babban limamin masallacin Juma’a na garin Kirikasamman, Ali Liman, ya koka kan yadda matasa suke maida sharholiya da gamayya tsakaninsu ruwan dare a jihar.

Ya gode wa karamar hukumar da ta bijiro da wannan doka domin ceto ‘ya’yan su da suka fada cikin mummunar hadari da zinace-zinace da daukar cikin da ba a yi shi cikin aure.

Share.

game da Author