Buhari ya nada sabon shugaban Hukumar Hajji ta Kasa

0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari Ya aika da sunan sabon shugaban hukumar Hajji Ta Kasa wanda zai canji Abdullahi Mohammed, majalisar dattawa a ranar Talata.

Baya ga sunan sabon shugaban, akwai sunayen sabbin kwamishinonin hukumar da zasu taya sabon shugaban aiki idan majalisa ta amince da shi da su duka.

Wanda aka nada sabon shugaban hukumar Hajji ta kasa shine Zikrullah (Sikiru) Olakunle Hassan daga jihar Osun. Hasan zai canji Abdullahi Mohammed.

Kwamishinonin da Buhari ya zabo sun hada da – Abdullahi Magaji Hardawa (Bauchi, North-East), Nura Hassan Yakasai(Kano, North-West) Sheikh Momoh Suleman Imonikhe (Edo, South-South).

Manyan ma’aikata na wucin gadi kuma sun hada da Mrs Halimat Jibril, Jihar Neja, Abbas Jato, Jihar Barno, Garba Umar, Jihar Sokoto, Ibrahim Ogbonnah Amah, Jihar Ebonyi, Sadiq Oniyesaneyene Musa, Jihar Delta da Mrs. Akintunde Basirat Olayinka, daga Jihar Ogun

Wakilan ma’aikatun gwamnatin Tarayya kuma sun hada da Shehu Dogo, Ma’aikatar Jiragen Sama, Nura Abba Rimi, Ma’aikatar Harkokin Waje, Rabi Bello Isa,Ma’aikatar Kudi, Zainab Ujudud Sheriff,Ma’aikatar Kiwon Lafiya, Aminu Bako Yarima, Hukumar Shige da fice ta Kasa da Ibrahim Ishaq Nuhu, Babban bankin Najeriya, CBN.

Share.

game da Author