Yayin da gwamnatin Najeriya ke ta shelar kokarin rage rashin aikin yi a cikin matasa, sai ga shi bankunan kasar nan sun kori ma’aikata har 2,929 tsakanin watan Yuli zuwa zuwa Satumba, 2019.
Wannan rahoton na cikin Kididdigar Harkokin Bankuna: Dalla-dallar Kudaden Shiga da Yawan Ma’aikata, wanda Hukumar Kididdigar Alkaluman Tattalin Arziki, NBS ta fitar a shafin ta na intanet.
Rahoton ya ce an zabge ma’aikatan bankuna su 2,920 tsakanin watanni uku na Yuli zuwa Satumba, 2019.
“Kafin a zabge yawan ma’aikatan, akwai ma’aikatan banki har 104,364 a Najeriya, ya zuwa watanni uku da suka gabata.
“Amma a yanzu bayan an kori 2,929, sauran ma’aikatan bankuna 101,435 su ka rage ke aiki a bankunan cikin Najeriya.
Wannan lissafi ya kara nuna cewa a 2019 yawan ma’aikatan bankunan kasar nan a 2018 su 102,821 ne.
Yawan su ya sake raguwa kenan da mutum 1,367 idan aka kwatanta da na 2019.
Daga Yuli zuwa Satumba, an yi hada-hadar kudade a bankunan Najeriya har sau milyan 800,201,498, na kwatankwacin kudade har naira tiriliyan 42.76.
Adadin kudaden da aka tura ta wayoyin hannu ne suka fi yawa, har naira tiriliyan 26.18 a cikin watan Yuli zuwa Satumba.
Wato kenan an tura zunzurutun kudade a wadannan watanni uku a adadin yawan tura kudade har sau 298,988,572.”