Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kori shugaban hukumar tara haraji ta Kasa, Tunde Fowler.
Buhari ya nada Muhammad Nami, wanda kwararre ne a harkar tara haraji.
Wannan sanarwa ta fito ne daga fadar shugaban kasa bayan karewa wa’adin shugabancin Fowler a hukumar.
bayan haka sanarwar ta ce a yi maza-maza a sauya wa darektocin hukumar wuraren aiki, wato ayi wa hukumar garanbawul.