A karshen wannan mako ne fitacciyar ‘yar wasar fina-finan Kannywood da ta yi fice ba a Arewa ba kawai harda fina-finan kudu ta shirya kasaitaccen biki na murnar zagayowar ranar haihuwar ta.
Wannan biki ya zo daidai da kaddamar da sabon gidan cin abinci da gyara jiki wato kwalliya da ta bude a garin Kaduna.
Rahama ta Burge kawayenta da wadanda suka hakarci wannan biki da irin kayar kasaita ta saka na (Yan gayu).
Ta shigo wajen wannan biki tana rangwada, sannan ta na taku yadi-yadi, a gefenta babbar kawarta kuma jaruma Fati Washa ta na binta suna takawa sannu a hankali suna tattaunawa.
Rahama ta yi bikin cikan ta shekaru 26 a duniya baya.
Baya ga ‘yan uwanta da suka halarci wannan taron biki, akwai wasu fitattun ‘yan wasan Kannywood da fitaccen Furodusa Yaseen Auwal duk sun halarci taron.
Abinci sai wanda kake so domin kuwa kai da kanka ne zaka garzaya teburin da aka jera su ka dibi abinda kake so kaci.
Baya ga nan Sadau ta yanka Kek dinta sannan da cashe tare da abokananta da yan’uwa.
Idan ba a manta ba Sadau da Fati Washa sun dan kwana biyu a kasar Birtaniya inda suka halarci bikin karrama jaruman fina-finai kasashen Afrika da aka yi a Landan a watan Nuwamba.
Sadau da Washa duk sun samu kyautuka a wannan karramawa.
Biki dai yayi armashi a garin Kaduna, anci, ansha sannan an cashe matuka.
A karshe ta gode wa masoyanta da baki sannan ta yi kira ga mutane su rika garzayowa suna hutawa a wannan sabon waje da ta bude, wato Sadau homez.