Kwamishinan kiwon lafiya na jihar Legas Akin Abayomi ya bayyana cewa gwamnati ta rufe manya da kananan shagunan siyar da magani 24 a fadin jihar.
Abayomi yace gwamnati ta yi haka ne domin dakile yadda jabun magunguna suka karade jihar.
Ya ce an kama wadannan shaguna ne da laiffukan da suka hada da saida magunguna a wuraren da basu da tsafta, bude shagon ba tare da lasisi ba,siyar da magani ba tare da kwararren masanin magani ba kwantar da marasa lafiya tare da karin ruwa da sauran su.
Abayomi yace gwamnati ta kai wannan samame shagunan ne tare da hadin guiwar hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC), rundunar ‘yan sanda, kungiyoyin masanana magunguna da sauran su.
Shagunan da aka rufe suna unguwannin Abule Egba, Alagbado, Kola, Meiran, Ekoro da Oko-Oba duk a kananan hukumomin Ifako Ijaiye da Alimosho.
Daga nan Abayomi yace gwamnati ba za ta yi kasa-kasa ba wajen ganin ta hana siyar da jabbun magnunguna sannan da hana wadanda basu da kwarewa a sanin maganin siyar wa mutane magunguna.
Ya kuma ce daga yanzu gwamnati ta kafa dokar hana duk ‘yan kasuwan da basu da lasisi siyar da magani a jihar.
A watan Oktoba ne kungiyar masana magungun ta kasa rashen jihar Jigawa (PCN) ya rufe manya da kananan shagunan saida magunguna 332 a fadin jihar.
Darektan sa ido na PCN Anthonia Aruya ta ce an kama wadannan shagunan magunguna ne da laiffukan da suka hada da rashin lasisin bude shago, siyar da magani ba tare da izinin ma’aikacin kiwon lafiya ko kuma masanin magani ba, rashin tsafta, rashin ingantaccen wurin ajiye magani.
Aruya ta ce kungiyar za ta ci gaba da gudanar da bincike domin ganin ta kawar da duk ire-iren wadannan baragurbin shagunan a fadin jihar.