Malamin jami’ar Ahmadu Bello, Adamu Chonoki da kanensa Umar Chonoki da shima malami ne a kwalejin kimiya da fasaha dake Kaduna sun kubuta daga hannun garkuwa da mutane da suka tsare su kwanaki da dadewa.
Kakakin kungiyar ‘yan jihar Kebbi mazauna garin Kaduna kuma Garkuwan Wakilin sarkin Zuru, Garba Mohammed ya sanar da haka.
Ya ce Adamu da Umar sun iso fadar sarkin Zuru da karfe 11:15 na safiyar Lahadi.
Idan ba a manta ba a kwanakin baya ne masu garkuwa da mutane suka yi garkuwa da Adamu. Bayannan sun bukaci iyalen Adamu su biya kudin fansa har Naira miliyan 2 da babur daya.
Kanin Adamu, watk Umar ne ya kai musu kudin sai dai bayan sun amshi kudin sai suka tsare shi. Suka bukaci ‘yan uwan su aiko da karin kudi naira miliyan 10 kafin su sake su duka.
Tun daga wannan lokaci Adamu da Umar na tsare a hannu wadannan masu garkuwa da mutane.
Masu garkuwa da mutanen su karbi Naira miliyan biyar daga hannun iyalin Chonoki sannan suka kara bukatan a biya su Naira miliyan 10.
Tun daga wancan lokaci, sai yan uwan Adamu da Umar suka sadaka, suka koma ga Allah.
Garba ya yi wa manema labarai, jami’an tsaro da dai sauran mutane godiya kan kokarin da suka yi wajen ganin Adamu da Umar sun dawo gida.
Kakakin yan sandan jihar Kaduna bai ce komai ba tukunna game da kubutar wadannan mutane.