Kungiyar likitoci na (NCS) ta koka kan yadda cutar hawan jini ke kama mutane a kasar nan.
Kungiyar ta koka da haka ne a taron samar da madafa kan yadda za a shawo kan yaduwar cutar a kasar nan da aka yi a jihar Enugu.
NCS ta ce bincike ya nuna cewa akalla kashi 30 bisa 100 na mutanen Najeriya na fama da cutar.
Binciken ya nuna cewa matasa musamman masu shekaru 25 na cikin yawa-yawan mutanen dake kamuwa da wannan cuta a kasar nan.
Kuma cutar na daya daga cikin cututtukan dake kisan mutane a duniya ganin cewa cutar na haddasa cututtukan dake kama zuciya, shanyewar bangaren jiki, yawan mantuwa, kawo bari ga mata masu ciki, cutar koda da sauran su
NCS ta yi kira ga mutane da su kiyaye hanyoyin guje wa kamuwa da cutar.
Wadannan hanyoyi kuwa sun hada da:
1. Mutum ya yawaita motsa jiki domin rage kiba a jiki
2. A rage yawan cin Kitse, sannan a yawaita cin kayan lambu da ganyayyaki.
3. A rage shan kayan zaki
4. A rage yawan cin gishiri.
5. Shan taba sigari da shan giya na kawo cutar hawan jini.
6. A yawaita zuwa asibiti domin yin gwaji akan cutar.