ATIKU KO BUHARI: Kotu ta wancakalar da karar Atiku

0

Kotun sauraren karrarakin zaben shugaban Kasa ta wancakalar da karar da Atiku ya shigar yana Kalubalantar zaben Buhari shugaban Najeriya.

Alkalin kotun Garba Mohammed ya ce PDP da dan Takaran ta basu bayyana kwararan hujjoji da ya nuna cewa ba Buhari bane yayi nasara a zaben shugaban kasa na 2019.

Idan ba a manta ba Atiku da PDP sun shigar da kara kwanaki 177 da suka gabata, a ranar 18 Ga Maris.

Kotun ta cika makil da dimbin masu mulki, wadanda suka ci zabe a karkashin APC.

Daga cikin su akwai Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Abba Kyari, Ministan Shari’a, Abubakar Malami, Ministan Ayyuka, Raji Fashola, Ministan Kwadogo Chris Ngige, Karamin Ministan Yankin Neja Delta, Festus Keyamo da sauran su.

Adams Oshimhole ne ya wakilci APC, yayin da Lauya Waleed Ahmed Sarki ya wakilci Shugaba Muhammadu Buhari.

Agbamuchi Mba ke wakiltar INEC, tare da lauya Yusuf Usman. Shi kuma Levi Uzuegwu, babban lauyan da ke wakiltar PDP. A cikin kotun har da Nuhu Ribadu, tsohon dan takarar gwamna da na shugaban kasa, kuma tsohon shugaban hukumar EFCC.

Shi ma shugaban jam’iyyar PDP, Uche Secondus da shugaban AIT, Raymomd Dokpesi duk su na cikin kotun.

Lauya Yusuf Abubakar ke wakiltar Atiku Abukar, yayin da Buhari da Atiku duk ba su cikin kotun. A yayin da ake yanke wannan hukunci dai Atiku ya na Dubai.

Baya ga daruruwan gungun lauyoyin bangarorin biyu na kuma wadanda suka je saurare don kashin kan su. Akwai gwamnoni da dama da suka cika kotun, ciki har da Atiku Baguru na Jihar Kebbi da Simon Lalong na Jihar Filato.

Dama kuma doka ta ce a tabbatar an yanke hukunci cikin kwanaki 180 bayan shigar da kara.

Share.

game da Author