A wata gwagwagwar da aka shafe sama yini guda cur ana karanto bayanan hukuncin karar zaben shugaban kasa na 2019, Kotun Daukaka Kara ta bai wa Shugaba Muhammadu Buhari nasara a kan abokin takarar sa, Atiku Abubakar na PDP.
Kotun Daukaka Karar Zaben Shugaban Kasa, ta kori karar da PDP da Atiku Abubakar suka shigar, inda suka kalubalanci zaben shugaban kasa da INEC ta bayyana cewa Buhari na APC ne ya yi nasara.
Alkalai biyar ne suka gudanar da shari’ar, a karkashin jagorancin Babban Mai Shari’a Mohammed Garba.
Atiku da PDP ba su yi nasara a kan bukatu biyar da suka roki kotun ta biya musu ba.
Garba Mohammed yayin karanto hukuncin sa, ya ce masu kara sun kasa gabatar wa kotu hujjojin da za ta gamsu da su, don haka ta yi fatali da karar.
Cikin batutuwan da kotu ta yi watsi da su har da batun zargin an gudanar da zabe a yawancin wurare ba bisa ka’idar da Dokar INEC ta shimfida ba, magudi, amfani da kudi, amfani da karfin jami’an tsaro, rikice-rikice da tashe-tashen hankula da sauran batutuwan da kotu ta ce duk PDP da Atiku sun kasa gamsar da kotu amincewa da zarge-zargen da suka yi.
Batun ‘Satifiket’ din Buhari
Kotun Daukaka Karar Zaben Shugaban Kasa ta yi watsi da ikirarin da INEC ta yi cewa karar da PDP ta shigar dangane da satifiket din Shugaba Buhari, batu ne na kafin zabe, ba bayan an rigaya an yi zabe ba.
INEC ta ce batun satifiket din bai kamata ya shigo a cikin wannan kara ba, kamata ya yi a ce tun kafin zabe PDP ya kamata ta kai batun kutu.
PDP ta tsaya kai da fata cewa Buhari bai cancanci tsayawa takara ba, domin ba shi da takaitaccen satifiket din da doka ta tanadar ya tsaya takarar shugaban kasa da shi.
Wannan na daga cikin batutuwa da yawa wadanda PDP ta yi amfani da su ta maka INEC, Buhari da APC kotu.
Sai dai shi kuma Shugaban Kotun, ya yi amfani da Sashe na Doka na 138 (1) (a) ta Dokar Zabe, inda ya ce sashin ya amince mai kara ya shigar da karar zargin abin da ya danganci gabatar wa INEC bayanai na karya.
“Don haka na amince da cewa wannan batu ba batu ba ne da ya tsaya a kana bin da ya danganci shari’ar abin da ya faru kafin zabe ba ne kawai.”
Garba ya ce don haka kotu za ta duba sahihanci ko akasin abin da ake kara akai.
Duk sauran alkalai hudu ba su yi tantamar wannan bayani ba.
An wanke Jami’an Tsaro daga Zargin Magudi
Kotun Daukaka Kara ta yi watsi da zargin da PDP ta yi wa jami’an tsaro cewa sun yi magudi, domin Shugaba Muhammadu Buhari ya kayar da Atiku Abubakar a zaben 2019.
Kotun ta yi watsi da wani bangare da PDP ta yi zargin cewa APC ta yi amfani da jami’an tsaro, inda suka hada kai suka yin walle-walle da zaben shugaban kasa na 2019.
Idan ba a manta ba, PDP ta zargi shugaba da ke kai, Muhammadu Buhari cewa shi da manayan hukumomin gwamnati da INEC din ita kan ta da kuma jami’an tsaro na da hannu wajen karkatar da zabe da kuma sakamakon zabe, domin Buhari ya yi nasara a kan Atiku.
Kotu a yau Laraba ta samu cikar a cikin korafin da PDP ta gabatar, yayin da INEC ta nuna wa kotu cewa kamata ya yi PDP ta bayyana sunayen jami’an tsaron da ta ke zargi a cikin karar ta da shigar.
Don haka kotu ta cire jami’an tsaro daga cikin wadanda ake zargi
Rashin Tsarma sunan Osinbajo cikin wadanda ake kara
A nan ma Kotun Daukaka Kara ta yi watsi da rokon da INEC ta yi cewa tunda PDP ba ta saka sunan Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ba, to a kori karar.
Kotu ta ce ai zaben ba a kan Osinbajo ya ke ba, a kan Buhari da kuma jam’iyyar da Buhari ke wakilta. Don haka babu wata damuwa ko kuskure don babu sunan Osinbajo a cikin wadanda ake kara.
A kan Atiku ba dan Najeriya ba ne
A nan ma kotu ta ce ita aikin ta shi ne ta duba cancantar cin zaben sa ko akasin haka. Shin ya ci da kuri’un da doka ta tanadar ko kuwa? Sannan dokar kasa ta 131 da ta 137 sun ce idan mutum dan Najeriya kuma ya cika shekara 40 da haihuwa, to shikenan.
Zargin wai Lauyan PDP ba cikakken Lauya ba ne
A nan ma kotu ta yi watsi da wannan zargi da INEC ta yi, inda ta ce a kwafe-kwafen takardun karar da aka shigar tun a ranar 18 Ga Maris, akwai tambarin sa hannun Kungiyar Lauyoyi ta Kasa cewa lauyoyin da ke cikin karar duk mambobin ya ne.
Don haka kotu ta ce ta amince Lauya Levi Uzoukwu lauya ne, kuma babban lauya.
Batun zargin Buhari ya yi amfani amfani da Kudi
Kotu ta yi watsi da wannan zargi da Atiku da PDP suka yi, inda suka ce an yi amfani da kudi ta hanyar Tradermoni, aka rika raba wa jama’a kudi domin su zabi APC da Buhari.
Lauyan Buhari ya kalubalanci wannan zargi da Atiku ya yI wa Buhari, inda ya kara da cewa ai Atiku da PDP bas u da hurumin yin wannan zargin raba kudi da suka ce Buhari yay i ta hannun mataimakin sa Osinbajo. Dalili, me ya sa bas u hada da sunan shi Osinbajo a cikin wadanda su ke kara ba? Wannan kenan.
Bayan dawowa daga hutun minti 40
An ci gaba da tattauna batutuwa akan ko mafiya yawan masu jefa kuri’a ne suka zabi Buhari ko a’a.
Ko zaben Buhari ya haramta saboda yawaitar magudi da ake zargin an yi ko a’a.
Ko zaben Buhari ya halasta saboda zargin yawaitar kin bin dokokin da INEC ta shimfida ko a’a.
Ko Buhari bai cancanta ba, saboda zargin tafka wa INEC karya a cikin takardun bayanan karatun sa ko a’a.
Matsayin Karatun Buhari a Kotu
Kotu ta yi amfani da Sashe na 131 na Dokar Kasa, ta ce ta amince Buhari ya sanar cewa ya na da takaitaccen zurfin ilmin da ake bukata ya tsaya takarar shugaban kasa.
Babu wasu hujjoji a gaban kotu da ke nuna cewa Buhari yay i wa INEC karya ko kuma ya shiga aikin soja ba da kwalin satifiket din kammala sakandare ba.
Kotu ta ce abinda dokar kasa ta ce dangane da shiga takara, shi ne dan takara ya kasance ya na da ilmin da ya mallaki takardar shaidar satifiket na wannan ilmin.
Sannan kuma Shugaban Alkalan ya ci gaba da cewa doka ba ta ce lallai said an takara ya manna satifiket din sa cikin bayanan INEC ba kafin ya cancanci tsayawa takara.
Kotu ta kara da cewa ‘satifiket’ din Buhari na aikin soja ya fi na san a kammala sakandare martaba da daraja.
Garba ya ci gaba da karanto bayanan da hukumar tsaro ta soja ta bayyana cewa satifiket din Buhari na hannun ta.
‘SATIFIKET’: Da Muhammad(U) Da Muhamm(E)d Duk Daya ne –Kotu
Kotun Daukaka Kara ta zartas da cewa Buhari ya cancanci tsayawa takara. Ba fa Buhari ne da kan sa ya buga wa kan sa ‘satifiket’ din ba. Kuma babu wata hujjar da ke nuna cewa sunan da ke cikin ‘satifiket’ din sa na WAEC daga Cambridge ba na sa ba ne.
“Ni dai ra’ayi na shi ne Muhammadu Buhari mai harafin ‘U’ a cikin sunan Muhammadu, shi ne dai Mohammed Buhari mai harafin ‘E’ a sunan Mohammed.”
Rumbun Tattara Bayanai: Dalilin Kotu ta yi fatali da zargin da Atiku ya yi wa INEC
Kotu ta ce PDP ta dogara ne da ‘ji-ta-ji-tar’ wata kafa dangane da matsayin da ta dauka a kan na’urar tattara bayanai, watau ‘server’, wadda ta yi zargin INEC ta tattara bayanan zabe a cikin ta.
Sannan kuma ta nuna cewa babu inda doka ta ce INEC ta yi amfani da ‘server’ wajen tattara sakamakon zabe.
Da ya ke karanta hujjojin da PDP ta gabatar wa kotu, inda ta yi ikirarin cin zabe, Garba, a madadin sauran alkalai, ya ce PDP ta kafa hujja da dalilan da masanin sinadaran intanet, mai suna Joseph Gbenga ya gabatar wa kotu, wadanda shugaban alkalan ya ce wannan ba abin kafa hujja ko karba ne a matsayin hujja ba.
Gbenga shi ne mai bada shaida na 60 da jam’iyyar APC ta gabatar.
Garba ya ci gaba da karanto cewa: “Gaskiya ba za a iya karbar Gbenga a matsayin wani gazagurun masanin dabarun sarrafa na’urori da alkaluma a intanet ba. Ya zo kotu ya yi rantsuwa da kan sa cewa shi fa ba wani kwararre ba ne.”
Atiku da PDP sun shigar da kara kwanaki 177 da suka gabata, a ranar 18 Ga Maris.
Saura jiran ko Atiku da PDP za su garzaya Kotun Koli ko za su hakura.
Dama kuma doka ta ce a tabbatar an yanke hukunci cikin kwanaki 180 bayan shigar da kara.
Nasarar Buhari a kan Atiku a kotu
Kotun Daukaka Karar Zaben Shugaban Kasa ta yi watsi da karar da dan takarar shugabancin kasa a karkashin jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar da ita kan ta PDP din suka kai karar APC da dan takarar ta, Muhammadu Buhari.
PDP da Atiku ba su yi nasara a batutuwa biyar da suka roki kotun ta yi musu ba, domin a kwace sakamakon zabe daga Buhari da APC a ba su.
Wannan ce kara ta hudu da kotun ta kora, bayan kafin yau, ta kori kararraki uku da wasu jam’iyyu suka kai a gaban ta, inda su ma suka kalubalanci nasarar da INEC ta bayyana cewa Buhari da APC sun yi a zaben shugaban kasa na 2019.
Yayin da sauran jam’iyyu ukun babu wadda ta nuna garzayawa Kotun Koli domin kalubalantar wannan hukunci, za a jira a ga ko Atiku da PDP za su garzaya Kotun Koli.
Jama’a da dama a yanzu za su zuba ido su ka ko Shugaba Muhammadu Buhari zai yi amfani da wannan dama wajen kara kaimi da jajricewa ya fuskanci kalubalen matsalolin da suka sha kan kasar nan.
PREMIUM TIMES HAUSA dai ba ta ji Arewacin kasar nan ya barke da murnar nasarar da Buhari ya samu a kotu ba, kamar irin yadda aka rika murna bayan ya lashe zaben 2015 da na 2019. Za mu ji dalili nan gaba.
Discussion about this post