Abubuwa uku da zan fi maida hakali a kai – Bande, Shugaban Zauren UN

0

Sabon Shugaban Zauren Majalisar Dinkin Duniya, Tijjani Bande, ya bayyana cewa zai fi maida hankali a kawar da yunwa da fatara, samar da ingantaccen ilmi da kuma jan sauran kasashe a jikin Majalisar Dinkin Duniya.

Haka Bande, dan Najeriya ya bayyana a wata tattaunawa da manema labaran Majalisar Dinkin Duniya ta yi da shi.

Ya jaddada cewa idan idan aka samar da ilmi mai inganci, hakan saisaita komai da kowa. Ya danganta alakar da ke tsakanin ilmi da kuma samar da aikin yi da daidaiton al’umma da kuma sanin ‘yancin su tare da ba su wannan ‘yancin.

“Duk wanda aka hana ilmi, to a hakikanin gaskiya an tauye masa komai na rayuwa.

Da ya ke magana a kan fatara, yunwa da talauci, Muhammad Bande ya ce idan har kasashe mambobin Majalisar Dinkin Duniya suka bayar da hadin kai, to za a samu gagarimin ci gaban kawar da kuncin rayuwa a cikin milyoyin al’ummar kasashen duniya.

“Ana bukatar kowace kasa ta gabatar da bayanan duk wani kokari ko yunkuri aka yi a kasar wanda ya yi tasiri da wanda bai yi ba, domin a sake nazarin yadda za a samu hanya daya mafita.”

Ya kuma nuna irin kokarin da za a yi domin rage gibin da ake samu wajen tazarar da ake bai wa kananan yara mata a fannin samar da ilmin zamani.

PREMIUM TIMES ta bada rahoton zaben da aka yi wa Bande a matsayin Shugaban Zauren Majalisar Dinkin Duniya, zama na 74 a ranar 4 Ga Yuli.

Zai rike wannan mukami ne tsawon shekara daya tare da zuwa majalisar cike da kudirin da ya dauko daga kasar sa Najeriya. Kasashen Afrika ne suka taru suka amince da shi, ba tare da nuna rashin amincewa daga wani. Sannan kuma sauran mambobin kungiyar ta UN ba su nuna wata ja-in-ja ba.

Dama kuma ya dade ya na aiki a majalisar.

Share.

game da Author