Ku daidaita wa ’Yan Sanda sahu –Gargadin Buhari ga Hukumar ’Yan Sanda

0

A daidai lokacin da matsalar tsaro ke kara tabarbarewa a kasar nan, Shugaba Muhammadu Buhari ya umarci Hukumar Kula Da Aiki ’Yan Sanda ta Kasa da ta inganta tsarin kare rayuka, dukiyoyi da lafiyar al’ummar Najeriya.

Buhari ya yi wannan kira ne a jiya Talata a Abuja, lokacin da ya ke karbar rahoton Hukumar Aikin Dan Sanda na 2018.

Daga cikin ikon da hukumar ke da shi har da nada shugabanni, karin girma da kuma ladabtar da jami’an ‘yan sandan Najeriya.

Cikin wata sanarwa da kakakin Buhari, Femi Adesina ya sa wa hannu, Buhari ya ce hukumar ta na da babban kalubale ne lura da al’amurran aikin dan sanda.

Amma kuma shugaban ya nuna cewa ya na da yakinin wadannan mambobi za su yi nasarar gudanar da aikin su yadda kwalliyar ‘Nes Labul’ za ta biya bukata a fannin tsaron kasar nan.

“Mutanen da ke cikin wannan hukuma akasari mutanen da na sani ne kuma wasun su ma sun san abin da harkar aikin dan sanda ke ciki. Don haka ina bukatar ganin kun daidaita wa aikin dan sanda sahu.

“Ina da yakinin cewa Sufeto Janar na ‘yan sanda na aiki mai kyau, ya na bakin kokarin sa. Amma duk da haka, idan ba mu daidaita sahun aikin dan sanda a kasar nan ba, to matsalar tsaro za ta ci gaba da zama a cikin halin jula-jula.

“Aikin da aka dora muku mai nauyi ne sosai. Ya na bukatar sadaukarwa matuka, musamman a wannan lokaci da kasar nan ke fuskantar matsalolin tsaro na cikin gida.”

Share.

game da Author