JIGAWA: Kotu ta hana Hakimi korar Fulanin da suka shafe shekaru 50 a rugar su

0

Kotun Daukaka Kara a Jihar Jigawa ta jingine hukuncin da Babbar Kotun Shari’a ta Dutse ta yanke, inda ta amince da korar da Hakimin Fagam ya yi wa wasu Fulani daga rugar su.

Wani Bafulatani ne mai suna Muhammadu Jingi ya daukaka kara ta hannun wasu lauyoyi biyu, Baffa Alhassan da Hafizu Abubakar.

Lauyoyin sun yi wa Jingi da sauran Fulanin aikin lauya kyauta, bayan da Hakimin na Fagam da ke cikin Karamar Hukumar Gwaram, Auwalu Adamu ya maka su kara a Kotun Shari’a, kuma aka ba Hakimin gaskiya.

Ya nemi kotu ta tayar da su ne bayan ya shigar da karar cewa sun ki biyar harajin ladar zama kasar sa da suke biya a duk shekara.

PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda kotu ta kori Fulanin daga rugar su, inda suka shafe shekaru kimanin 50 su na zaune.

A can baya, Kotun ta Shari’a ce ta Gwaram ta umarci Fulanin su tashi daga rugar da suke zaune, wadda ke karkashin masarautar Hakimin Fagam, cikin Karamar Hukumar Gwaram, a Jihar Jigawa.

Sai dai kuma a yayin da alkalin Kotun Babbar Kotun Shari’a ta Dutse ke yanke hukunci, ya ce kotun Gwaram ba ta da hurumin korar Fulanin daga mazaunin su.

Mai Shari’a ya bayyana cewa: “Dukkan Masarautun Jihar Jigawa biyar an kirkiro su ne a karkashin dokar Kananan Hukumomi mai lamba L8 ta Jihar Jigawa. Kuma wannan dokar ce ta kafa Masarautar Dutse, wadda Gundumar Hakimin Fagam ke karkashin ta.”

Daga nan sai mai shari’a ya bayyana cewa Sashe na 64 na Doka ya bayyana wanda ke da hakki da kula da batutuwa kasa ko ganaki suke. Inji Alkali Sadiq.

Bayan kammala shari’a, sai lauyan masu kara, Hafizu Abubakar ya bayyana wa manema labarai cewa shari’a ta yi adalci sosai.

Shi kuma Jingi, Bafulatanin da ya shigar kara, ya bayyana jin dadin sa dangane da yadda shari’ar ta kaya. Ya ce shi bai san abin da aka tattauna a kotun ba, domin ba Turanci ya ke ji ba. Ya dai ji kawai mai shari’a ya ambaci sunan sa.

Daga nan sai ya ce ya yi farin ciki, domin yanzu tunda kotu ta ba su gaskiya, zai je ya ci gaba da gudanar da hakokin rayuwar sa a matsugunin su, bayan shekara biyu da komai ya yi cak, saboda shari’ar da aka rika tabkawa bayan umarnin tada su da aka bayar a kotun farko.

Share.

game da Author