Hukumar kula da jin dadin masu yi wa kasa hidima (NYSC) ta bayyana cewa masu bautar kasa uku sun rasu a hadarin mota a Katsina.
Kakakin hukumar Alex Obemeata ya sanar da haka a garin Katsina ranar Lahadi.
Obemeata yace masu yi wa kasa hidiman sun gamu da ajalinsu ne a hadarin mota da suka yi a karamar hukumar Kankara a hanyarsu na zuwa Funtuwa.
“ A ranar 18 ga wannan wata wasu kiristoci ‘yan darikan Katolika su 12 suka yi hadarin mota a karamar hukumar Kankara suma a hanyarsu na yayin da suke hanyar na zuwa taro a Funtuwa.
“ Nan take dai mutun uku suka rigamu gidan gaskiya sannan sauran duk sun samu rauni a jikinsu.
Ya ce hadarin motar ta auku ne a daidai gwamnan jihar Aminu Masari na kan hanyar a Gobirawa dake karamar hukumar Kankara.
Gwamna Masari ya bada motarsa daya cikin jerin motocin dake biye da shi domin a kwashe mutanen da suka ji rauni da gawan wadanda aka rasa zuwa asibiti.
Babban Kodinatan NYSC na jihar Ahidjo Yahaya ya ziyarci wadanda suka ji rauni a asibiti. Sannan ya yi wa iyaye da sauran masu yi wa kasa hidama ta’aziyar rasuwar wadanda aka rasa.
Discussion about this post