A taron tunawa da tsohon ministan Kiwon Lafiya Babatunde Osotimehin kungiyar ‘Academy for Health Development (AHEAD)’dake karkashin ‘PACFaH@Scale project’ ta shirya taro domin inganta hanyoyin samar da dabarun bada tazarar iyali a Najeriya.
Taron ya gudana ne a Ibadan jihar Oyo kuma ma’aikatan kiwon lafiya, kungiyoyin bada tallafi da wakilan gwamnati na daga cikin mutanen da suka halarci wannan taro.
Uwargidan Babatunde,Olafunke ta yaba wa Cibiyar ‘AHEAD’ kan girmama mijinta da suka yi ta hanyar ci gaba da kamfen don inganta kiwon lafiyar mata a kasar nan da Osotimehin ya fara.
Olafunke ta yi kira ga malaman makarantun boko da iyaye kan wayar da kan ‘ya’ya mata game da al’amirori da dawainiyar haihuwa.
Jami’i a ma’aikatan kiwon lafiya ta ƙasa Kayode Afolabi ya bayyana cewa gwamnati a shirye take domin hada hannu da Cibiyar AHEAD don ceto rayukan mata a kasar nan.
Afolabi yace burin ma’aikatar kiwon lafiya shine inganta kiwon lafiyar mata da yara kanana.
Shi kuwa Emmanuel Otorin ya koka da yadda mata kalilan ne ke iya samun dabarun bada tazaran iyali a kasar nan.
Ya ce sakamakon bincike ya nuna cewa mata kashi 13.9 bisa 100 ne ke iya samun dabarun bada tazaran iyali.
Bayanai sun nuna cewa tsakanin watan Yulin 2017 zuwa 2018 gwamnati ta yi nasarar kare mata miliyan biyu daga daukan cikin da basu so da kare mata 735,000 daga zubar da cikin da zai iya cutar da mai ɗauke da shi.