Magoya bayan Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da a Turance a ke kira Islamic Movement of Najeriya, ko kuma Harkar Musulunci a Najeriya, ta maida wa Fadar Shugaban Kasa kakkausan martanin cewa babu yadda za a yi Shugaba Muhammadu Buhari ya tsame kansa daga tsare jagoran na su.
Cikin wata takarda da kakakin yada labarai na IMN, Ibrahim Musa ya fitar, ya bayyana cewa:
“Muzaharorin da muke gudanarwa a kan titunan babban birnin tarayya, Abuja, muna yin su ne saboda nuna rashin yardarmu da kuma amincewarmu dangane da matakin da gwamnatin Nijeriya ta dauka na kin zartar da umarnin da babbar Kotu da ke Abuja ta bayar na a Saki Jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya daga haramtacciyar tsarewa ta zalunci da gwamnatin Nijeriya take yi masa wai da sunan “Tsarewa ta bayar da kariya”. Akalla kafin aiwatar da kisan kiyashin Zariya wanda aka kaddamar a cikin Watan Disambar 2015, titunan cikin garin Abuja wadanda suka fi daraja da kima a idon gwamnati fiye da rayukan ‘yan kasa ba su fuskanci ‘mamayar’ ‘yan’ uwa musulmi na Harkar Musulunci a Nijeriya ba.
“Babu yadda za a yi a iya tsame hannun Shugaban Kasa Muhammadu Buhari dangane da kisan kiyashin da Sojojin Nijeriya suka kaddamar kasancewarsa Kwamandan Askarawan Tarayyar Nijeriya, lamarin da ya sabbaba kisan ‘yan uwa Musulmi na Harkar Musulunci a Nijeriya, ‘yan kasa fararen hula wadanda ba su dauke da makami sama da dubu daya, wadanda suka hada da maza, mata da kuma kananan yara a tsakanin ranekun 12-14 ga watan Disambar Shekarar 2015.
“Gwamnati ta shelanta cewa ta aikata haramtaccen aiki na rufe gawawwakin ‘yan uwa Musulmi na Harakar Musulunci a Nijeriya guda 347 a cikin kabari na bai – daya a makabartar da ke kauyen Mando a cikin garin Kaduna bayan kaddamar da wannan mummunan kisan dimbin jama’a, lamarin da ya saba wa kudurin yarjejeniyar Geneva, da ma sauran dukkanin dokokin kasa.
“Kuma gwamnatin Tarayyar Nijeriyar ta ki yin aiki da umarnin da Hukumar Bincike ta bayar na kamawa tare da hukunta Sojojin da suka kashe mutane masu son zaman lafiya ‘yan uwa Musulmi na Harkar Musulunci a garin Zariya.
“A cikin watan Disambar 2016 babbar kotu da ke Abuja ta yanke hukuncin a saki Shaikh Zakaky da mai dakinsa, Malama Zeenah daga haramtacciyar tsarewa ba bisa ka’ida ba da ake yi masu, a biya su diyya ta Naira Miliyan 50, a kuma gina masa gida a duk inda yake so a fadin Arewacin tarayyar Nijeriya tare kuma da samar masa da kariya ta jami’an tsaro.
“Gwamnatin Shugaban Kasa Buhari ta yi fatali da wannan umarni na Kotu, ta kuma ki mutunta alfarmar Kotu da kuma Alkalai. To don haka wace kotu ce kuma Shugaban Kasa yake maganar a bari ta bayyana matsayin Jagoranmu?”
Idan ba a manta ba, karshen makon jiya na dai Fadar Shugaban Kasa ta bayyana cewa shari’ar El-Zakzaky ba a hannun Buhari ta ke ba
Fadar Shugaban Kasa ta bayyana cewa shari’a ko tuhumar da kuma ci gaba da tsarewar da ake wa Shugaban Mabiya Shi’a, Ibrahim El-Zakzaky, ba laifin shugaban kasa ba ne.
Kakakin Shugaba Muhammadub Buhari, Garba Shehu ne ya bayyana haka a jiya Juma’a, a cikin wata takardar da ya fitar wa manema labarai.
Malamin ya na fuskantar shari’a ne a Kaduna, sanadiyyar rikicin da ya biyo bayan tare hanyar da mabiyan sa suka yi wa sojoji a cikinn watan Disamba, 2015.
Wannan ya haifar da mummunan kisan da sojoji suka yi wa mabiyan sa a lokacin.
Shi ma an ji masa ciwo tare da matar sa Zeenat sanadiyyar harbin da ya samu bayan da aka kai wa gidan sa hari.
Sannan kuma an kashe masa ‘ya’ya uku a lokacin mummunan rikicin.
Duk da umarnin da kotu ta bayar, har yau ba a sake shi ba saboda wasu dalilai wadanda a baya gwamnatin tarayya ta bayyana.
Sai dai kuma Fadar Shugaban Kasa ta shawarci mabiya malamin da su daina fitowa kan titina su na tayar da hankulan jama’a domin neman a saki jagoran su.
Garba Shehu ya bayyana cewa kamata ya yi su maida hankali a kotu inda a ke ci gaba da shari’a, domin batun sa ya na kotu, ba a hannun shugaban kasa sa.
Ya ce mabiya malamin ba su da wani izni ko fifikon fitowa sun a yadda suka ga dama tare da take doka da sunan zanga-zanga.
Ya ce wadanda suke takurawa a lokacin zanga-zanga, ta hanyarctarec hanyoyi, su ma su na da ‘yancin yin zirga-zirga, ba tare da wani ya tare musu hanya ba, kamar yadda mabiya malamin ke yi.
Sanarwar ta kuma kara da cewa ba fa kowace gwamnati ba ce za ta iya zura ido ta na kallon yadda wasu ke lalata dukiyoyi da kawo wa zamantakewar wasu masu bin doka da oda barazana da sunan zanga-zanga.
Ya ce Shugaba Buhari ba ya yi wa kotu katsalandan cewa a saki wani ko a daure wani.
Daga nan ya ce su bi ba’asin shari’ar El-Zakzaky a kotu, ba hannun Buhari ba, tunda ba Shugaban Kasa din ne ya tsare shi ba.
Sai dai kuma wannan magana daga fadar ta shugaban kasa ta sa Ibrahim Musa maida martani, inda ya ci gaba da cewa: “saboda iya makirci, sai ga shi gwamnati ta shigar da wata sabuwar kara a gaban wata kotu a garin Kaduna, shekaru uku bayan kisan kiyashin Zariya, wai ana zargin Jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya wanda aka harbi mai dakinsa, aka kashe masa ‘ya’ya uku, aka kona yayar sa da dan wan sa da wuta da ransu, bayan shi kuma an harbe shi a wurare da dama a jikinsa, wai ana tuhumarsa da laifin kisan kai.”
“Wannan ya biyo bayan hukuncin da da babbar Kotun Jihar ta Kaduna ta yanke na sakin ‘yan’uwa Musulmi na Harkar Musulunci a Nijeriya sama da dari daya, lamarin da ke tabbatar da cewa, kawai ana so ne a ci gaba da barin Jagoranmu cikin yanayi na Haramtacciyar tsarewa ba bisa ka’ida ba.
Daga karshe ya bayyana cewa, “ci gaba da tsare Shaikh Zakzaky duk kuwa da ci gaba da tabarbarewa da halin lafiyarsa ke yi aiki ne na azabtarwa tare kuma da jiranya rasa ransa, da nufin haifar da barkewar mummunan tashin hankali a kasa da sunan Harkar Musulunci a Nijeriya. Don haka idan ana so a karyata wannan batu, to gwamnati ta saki Shaikh Zakzaky.”