Mata ta daba wa mijinta wuka a tsakiyar zuciya

0

Wata mata ‘yar shekara 20 ta daba wa mijinta mai shekaru 35 wuka a tsakiyar zuciyarsa.

Matan mai suna Makoduchukwu Ndubisi ta daba wa mijinta Johnbosco Nguwukan ne bayan sun kaure da rikici a gidan auren su.

Kakakin ‘yan sandan jihar Anambra Haruna Mohammed ya ce tuni har ‘yan sanda sun aika da gawan Johnbosco Ngu dakin ajiya gawa dake Asibitin garin.

Sai dai kuma Haruna ya ce har yanzu ba a tantance ainihin abin da ya hada su da har ya kaiga ta kashe mijin nata ba.

” Har yanzu dai ana nan ana gudanar da bincike a kai.

Share.

game da Author