Najeriya da kasashen Yankin Afrika ta Yamma za su fara amfani da kudi na bai daya

0

Kasashen yankin Afrika ta Yamma sun saka hannu a takardar amincewa da fara amfani da kudi na bai daya mai suna ECO.

Wannan amincewa ya biyo bayan tari. Da kungiyar raya yankin kasashen Afrika ta Yamma da ya gudana a Babban Birnin Tarayyan Najeriya, Abuja.

Kasashen sun hada da Benin, Burkina Faso, Cape Verde, Côte d’Ivoire, Gambia, Ghana, Guinea, Guinea-Bissau, Liberia, Mali, Niger, Nigeria, Senegal, Sierra Leone, Togo.

A jawabinsa, babban Sakataren ma’aikatan kasashen wajen Najeriya, Mustapha Suleiman, ya bayyana cewa kungiyar zata shirya tsari ta yadda za a fara amfani da kudin da sashen hada-hadar kudi da tsare-tsare na kungiyar.

Sabon shugaban kungiyar ECOWAS din kuma shugaban kasar Nijar, Mahammadou Issofou ya bayyana cewa kasashen da suma kammala shiri da game da fara amfani da kudin na bai daya zasu fara kai tsaye daga watan Janairun 2020.

” Kasashen da suka kammala shiri don fara amfani da wannan sabon tsarin kudi na bai daya zasu fara daga 2020, amma kuma kasahen da basu kammala shiri ba za su iya shiga shirin daga baya.

Sannan ya roki shugabannin kasashen da su maida hankali matuka domin samun nasara ga abinda suka sa a gaba.

Share.

game da Author