Kakakin Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa reshen jihar Osun (FRSC) Bisi Kazeem ya bayyana cewa an sako ma’aikatan hukumar biyu da aka yi garkuwa da su.
Kazeem ya bayyana haka ne wa PREMIUM TIMES ranan Laraba.
Ya ce masu garkuwan sun sako Abioye and Bayegunmi a daren Talata amma kuma babu tabbacin ko an biya kudin fansa kafin aka sako su.
Idan ba a manta ba a ranan Talata ne Hukumar FRSC reshen jihar Osun (FRSC) ta bayyana cewa wadanda suka yi garkuwa da ma’aikatan hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa su biyu sun nemi a biya Naira Miliyan daya kudin diyyan su kafin su sake su.
PREMIUM TIMES ta bada labarin yadda wasu masu garkuwa da mutane suka sace Bayegunmi da Abioye ma’aikatan FRSC a hanyar Iwaraja dake karamar hukumar Oriade ranan Litini.
Kakakin FRSC Bisi Kazeem da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Folashade Odoro suka tabbatar wa ‘yan jarida da haka.
A sakon da ya aika wa manema Labarai ranar Talata Kazeem ya bayyana cewa maidakin daya daga cikin ma’aikatan da aka yi garkuwa da su ta bayyana cewa masu garkuwan sun kira ta sannan sun bukaci a aika musu da Naira miliyan daya kafin su saki mijinta.
” Masu garkuwan sun bukaci da a biya wadannan kudade a yau Talata da karfe tara na safe.”
Garkuwa da mutane da karban kudaden diyya ya zama ruwan dare a Najeriya.
A cikin kwanakin nan ne wasu masu garkuwa da mutane suka saki wani farfesan jami’ar Awolowo dake Ile -Ife bayan an biya kudin diyyar sa.
Sannan a jihar Ekiti wasu masu garkuwa da mutane sun sace mutane uku ranan Lahadi inda suke bukatan a biya su kudin diya sama da Naira miliyan 20.