Ana bukatan gina dakunan bahaya Miliyan 2 Najeriya duk shekara – UNICEF

0

Bisa ga sakamakon binciken da asusun kula da al’amuran yara kanana na majalisar dinkin duniya (UNICEF) ta fitar ya nuna cewa mutane miliyan 47 na bahaya a waje a Najeriya.

Domin samun nasara a manufar tsaftace muhalli nan da shekara 2019 zuwa 2025 UNICEF ta ce Najeriya za ta bukaci karin ban dakuna miliyan biyu duk shekara na tsawon shekaru bakwai.

Jami’in UNICEF da WASH Bioye Ogunjobi ya bayyana haka a taron wayar da kan mutane game da mahimmancin tsaftace muhalli da illar yin bahaya a waje da aka yi a Abuja.

Taken taron shine ‘Tsaftace Najeriya;yi amfani da bandaki’ sannan UNICEF,WASH da ma’aikatar yada labarai ne suka shirya taron.

Ogunjobi ya yi kira ga gwamnati da ta maida hankali gina dakunan bahayan da ta ce zata yi a fadin kasar nan yana mai cewa akalla miliyan biyu a duk shekara ne zai iya warware matsalar yin ba haya da mutane ke yi a waje.

Ilollin rashin tsaftace muhalli.

Ogunjobi ya bayyana cewa rashin tsaftace muhalli na sa a kamu da cututtuka da ya hada da amai da gudawa.

Ogunjobi yace domin kauce wa matsaloli irin haka ya kamata gwamnati ta wayar wa mutane kai bisa sanin mahimmancin tsaftace muhalli da gina ban dakuna.

Share.

game da Author