Dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar , ya bayyana dalilin da ya sa ya ce bai amince da Zainab Bulkacuwa a cikin kwamitin alkalan ba.
Atiku yace dokar dan adam ta ‘common law’ ta ce bai yiwuwa mutum ya zama alkakin kan sa.
Ya ce don haka kiran da lauyoyin sa suka yi na Zainab ta sauka, an yi shi ne saboda kusancin ta daga daga cikin Jigon APC, Alhaji Adamu Bulkachuwa, wanda a yanzu haka zababben sanata ne.
Atiku ya kara da cewa kin amincewa da Zainab din da lauyoyin sa suka yi, ba ita kankin kan ta ko kimar ta ko nagartar ta ko cancantar ta ake yi ba.
Ya ce ya na girmama ta, kasancewar ta wadda ta fara assasa ganin an dabbaka daidaiton jinsi da kuma inganta rayuwar mata.
Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku, ya ce ya na ganin kimar Zainab kuma ya na ba ta girman ta.
“A kan haka na ke jinjina wa Babbar Mai Shari’a Bulkachuwa saboda janyewar da ta yi daga Shugabancin Kotun Sauraren Kararrakin Zaben Shugaban Kasa.
“Hakan da ta yi ya nuna irin kishin kasa da ta ke da shi. Sannan kuma hakan ya nuna jama’a za su kara karfafa amannar su a kan bangaren shari’ar kasar nan.
“Ba wai yabo da jinjina kadai na ke yi mata ba, ina kuma yin addu’a, musamman a cikin wannan wata na Ramadan, cewa kotun za ta yi adalci tare da sa tsoron Allah, ba wai ta yi duba ga biyayyar ta ga masu kan mulki a yanzu ba.
“Allah ya albarkaci sashen shari’ar mu, kuma ya albarkaci Najeriya.”
Discussion about this post