NYSC ta yi sabon shugaba

0

Hukumar Tsaron Sojoji ta Najeriya ta bada sanarwar nada S. Ibrahim a matsayin sabon Darakta Janar na Hukumar Kuda da Masu Aikin Bautar Kasa (NYSC).

Jiya Juma’a ne aka yi sanarwar nada Ibrahim, inda Kakakin Yada Labarai na sojoji, Sagir Musa ya ce shi Birgadiya Ibrahim ne ya canji S.Z Kazaure.

An dauko shi ne daga Jami’ar Sojoji da ke Biu, Jihar Barno.

Ba wannan ne kadai canje-canjen mukamai da aka yi wa manyan sojojin ba.

An yi wa da dama canjin wuraren aiki, ciki har da Birgediya B.A Dantsoho, wanda aka dauke daga Bangaren Dangantaka Tsakanin Fararen Hula da Sojoji zuwa Cibiyar Koyon Yaruka da Harsuna ta Sojoji
Shi kuma S.S Ibrahim shi ne Babban Rajistara na Jamai’ar Sojojin Najeriya da ke garin Biu, Jihar Maiduguri.

Tun da aka kafa Hukumar Kuda da Masu Bautar Kasa, wato NYSC, har yau sojoji ne ke shugabantar ta.

Maharazu Tsiga shi ya sauka kafin Kazaure, wanda a yanzu aka sauya shi da Ibrahim.

Share.

game da Author