Kungiyar Manchester United, wadda ya zuwa wannan mako, ta buga wasa 9 a jere, amma ta yi nasara a wasanni 2, an ci ta a wasanni 7 a cikin 9 din.
Ta na fama da gagarimar matsala, ko a ce matsaloli biyar wadanda kuma babu wata hanyar iya gagance su, kamar yadda masu sharhin wasan kwallo na Ingila da duniya ke nunawa.
Kafin Barcelona ta fitar da Manchester United a wasan Champions Legue, sai da Everton ta zura mata kwallaye 4:0.
Sannan kuma a ranar Talatar da ta gabata, Manchester City ta je har gida ta lallasa United da ci 2:0.
BABU SHIRIN GARAMBAWUL NA KUSA KO NA NESA
Babu wani takamaimen tsari ko shiri na tafiyar da kungiyar, ko kuma yin garambawul, tun bayan tafiyar dadadden mai horaswar kungiyar, Sir. Alex Ferguson.
A lokacin Ferguson, Manchester United ba ta bukatar dogon shiri idan ta sa gaba wajen neman nasara a gasanni kwallo.
Ferguson zai dora wakilcin gudanar da wasu ayyuka ga wadanda ya san za su iya, sannan kuma ya kan maida himma ya fuskanci kalubalen da ke gaban sa.
Ya san irin ’yan wasan da zai dauka masu jini a jika da za a ci moriyar su yau, gobe har zuwa shekaru sama goma a can gaba.
Matsala:
Matsaloli sun bijiro, sun lullube Manchester tun bayan tafiyar Ferguson, lokacin da Mataimakin Shugaban Kungiyar, Ed Woodward ya jagoranci tafiyar da sha’anin gudanarwar ta.
Sai ya rika tafiyar da Manchester kamar harka ta kwangila. Woodward bai san komai ba a harkar kwallo, amma sai ya kankame komai sai shi, sai kuma abin da ya ce kawai.
Nan da na sai aka fara yin kutubalbal da Manchester United, inda David Moyes ya karba ya ba Louis van Gaal. Shi kuma ya karba ya mika wa Jose Mourinho.
Dukkan su ukun babu wani wanda ya kamo hanyar da Ferguson ya bi ya dora kungiyar a hanyar kwallon kafa madaidaiciya.
Yanzu an kawo Ole Gunnar Solskjaer, wanda tsohon dan wasan kungiyar ne, ya san makama, kuma ya san madafa, amma kuma ba shi da masu dafa masa da zai iya taka tudun-mun-tsira har ya tserar da Manchester daga halin da ta ke a ciki.
RASHIN SAYEN KWARARRUN ‘YAN WASA
Dukkan kociyan da aka yi bayan Ferguson, ba su nuna kwarewa wajen sayen kwararrun ’yan wasa ba, sai su ka karkata wajen sayen wadanda suka sani kawai.
Sannan kuma sun rika samun sabani da wasu ’yan wasa, wadanda duk iyawar ka, idan ka na da matsala da kociya, to kai za ka kwan a ciki.
Duk kociyan da ya zubar da girman sa har ya ke fada da dan wasa, to ba kociyan kwarai ba ne.
Kowane kulob na Ingila da sauran kasashe na da tsarin daukar ’yann wasa da kuma tsarin salon wasan da suke takawa. Amma kuma kowane kulob na da wadanda ba su dace da irin salon wasan kulob din ba.
Amma wadanda ba su dace da Manchester ba, kuma su ke buga wasa a kulob din, sun fi na sauran kungiyoyi manya yawa.
Idan Manchester ba ta tashi tsaye ta gina tsarin da zai rike kungiyar tsawon shekaru 10 zuwa 20 nan gaba ba, to za su ci gaba da harbat-ta-Mati ne kawai. Sai dai su rika ganin wasu kungiyoyi na buga Champions Legue kawai, su kuma sun shiga rububi.
Ku dubi yadda tuni Gordiola na Manchester City ya daidaita da Gabriel Jesus, Raheem Sterling da Bernando Silva sun sabunta yarjejeiyar ci gaba da zama kulob din.
Amma Mancher United sai kwan-gaba-kwan-baya ta ke ta yi da Alixes Sanchez, wanda ke neman sai a biya shi albashin fam milyan 20.35 a duk shekara, duk da cewa ba ya tabuka komai a yanzu.
Idan Manchester ba su saki Sanchez ya tafi ba, to ba za su fita cikin matsalar ’yan wasa ba. Bai yiwuwa su rike shi suna biyan sa abin da ya fi sauran ’yan wasan da suka fi shi kokari, nesa ba kusa ba.
To amma wane kulob ne zai sayi Sanchez a yanzu? Wa zai sayi biri a sama, ko kuma jibadau-kayan-nauyi?
Sannan da wahala David de Gea da Marcus Rashford su sake zama kulob din idan wa’adin su ya cika.
MATSALAR MAI HORASWA
Ole Gunner da aka dauko, bai taba horas da wani babban kulob ba. An dai dauko shi ne domin a gaggauta cike gurbin da aka cire Mourinho, sannan kuma babu wani babban kociya da za a dauka a lokacin.
Ya na zuwa sai ya taki sa’a, kulob din ya koma cin kwallaye da samun nasara, ba kamar irin rikon-sakainar-kashin da Mourinho ya yi masa ba.
’Yan wasan da suka rika rigima da Mourinho, irin Rashford, Pogba, Anthonu Martial duk sun samu ’yancin su kenan. Sai dai kuma tun kunnen doki 2:2 da Manchester ta buga da kungiyar Burnley a cikin Janairu, shikenan sai hannun agogo ya rika komawa baya-da-baya.
RASHIN IYA TAKUN WASA
Manchester da ke hannun Solkjaer a yanzu ba ta da bambanci da wadda ya gada, babu abin da ya canja.
Karfin da ta ke takama da shi, shi ne karfin kwararren mai tsaron gida, De Gea da kuma karfin ‘yan gaba guda biyu kawai. Daga ba su ba kuwa, duk sauran magen-Lami ce, ba cizo ba yakushi.
Daga inda ka ce Manchester ta samu matsala daga masu tsaron bayan ta, to shi kuma mai tsaron gida sai duka ya yi masa yawa, har ya rasa wanda zai kare, a yi ta sharara masa ruwan kwallaye.
GAGGAWAR AMINCEWA DA SOLKJAER
Manchester ta yi gaggawar damka wa Solkjaer kwangilar tsawon shekaru uku. Ganin ya shigo da sa’a daga farko, an ci gaba da dora laifin matsala a kan Mourinho da aka kora.
Yanzu kuma da reshe-ya-juye-da-mujiya, sai ake dora laifin a kan ’yan wasa. Amma kuma ’yan wasan da Mourinho din ya bari, su dai ne har yanzu, ba a canja ko an kara ko daya ba.
MATSALAR GLAZER, MASU KUNGIYAR MANCHESTER
Idan aka koma duba matsalar da su kan su shugabannin Manchester ke haifar wa kulub din, to batun yawan kuskuren da De Gea ke yi idan an takura shi, ko surutan kwallo ba ta yi wa Pogba kyau a wani wasa ba, wannan duk karamar magana ce.
Manchester dai ta na karkashin wasu ’ya’yan hamshakin attajirin nan Malcolm Glazer, su shida ke da kulob din. Tun da suka sayi kulob din cikin 2005 su ke ta kwasar ribar da ake samu a duk shekara, su da sauran masu kananan hannayen jari a kulob din.
Daga 2005 zuwa bana, an cire fam bilyan 1, sama da naira bilyan 430 kenan daga asusun Manchester, ana biyan masu kulob matsayin ribar da ake samu a duk shekara.
Kamata ya yi wadannan makudan kudade a bar su a cikin asusun kungiyar ana kara mata karfi, kamar yadda irin su Real Madrid da Barcelona ke yi da kuma PSG da Manchester City su ke yi a yanzu .
Amma duk ribar da Manchester ta ci a karshen shekara, sai a kwashe kudin a tura birnin Florida na Amurka, inda shugabannin kungiyar ke zaune su na gudanar da harkokin kasuwancin su.
TULIN BASHI MAI WAHALAR BIYA
Ya zuwa karshen shekarar da ta gabata, ana bin Manchester bashin fam milyan 495.8. wanda dalilin wannan bashi ne shugabannin kungiyar a kashen kakar wasan da ta gabata suka rattaba ka’idojin cewa:
“Za mu rage yawan kashe kudade domin mu samu mu rika biyan bashin da ke kan mu. Cikin abubuwan da za mu kage kashe kudi a kai, har da yawan dauko haya ko sayen ‘yan wasa, rage yawan masu taimaka wa kociya….duk da dai mun san wannan zai shafi karfin iya gogayyar mu da sauran manyan kulob wajen samun ’yan wasa da masu horas da su.”
A lokacin da su Glazer suka sayi Manchester, sun taras da bashin fam milyan 275 a kan kungiyar.
Matsala ita ce, idan ba a biya bashin ba, to duk shekara akwai kudin ruwa har fam milyan 60 da zai rika karuwa, ko kuma a rika biya, har zuwa shekarar da aka biya kudin bashin gaba daya.
Irin yadda Manchester United ta rika samun makudan kudaden shiga, har yadda ta ke ci gaba da samu a yanzu, babu dalilin da zai sa a ce ba ita ba ce ta fi kowace kungiya karfi a duk duniya?
Shin wai me ya ake neman bari Manchester United ta koma ’yan-harbat-ta-Mati ne?
Sun samu kwararren kociya, Alex Fersguson, wanda ya sayar da Cristiano Ronaldo, ya sayi Micheal Owen arha takyaf, kuma a ci kofin Premier a shekarar. Idan ba Ferguson ba, duk duniya wane kociya ne zai iya yin haka?
HALIN DA OLD TRAFFORD YA KE CIKI
Yanzu idan ka ziyarci filin wasa na Old Trafford, haushi da takaici zai kama ka, idan ka ga yadda aka bar wasu sassa na sa ba a kula da su.
Ko a ranar Laraba ta makon jiya, sai da ruwan sama ya rika zubowa a kan ’yan kallo daga wani wuri da rufin filin ya lalace ba a gyara ba.
Sannan kuma sama da shekaru uku kenan narka-narkan beraye ke ta karakaina kuma su na ci gaba da yawa a cikin ginin filin kwallon.
Akwai wawakeken fili a cikin harabar filin kwallo nan a Old Trafford, wanda har yanzu an ki amfani da wurin a yi wasu gine-gine. Sai fa wani otal da ’yan wasan Mancherter wadanda suka ci kofi a 1992 suka hada kudi suka gina a filin.
Zamani ya zo duk wani babban kulob ya na tafiya da zamani, kuma ya na ci gaba. Madrid na kan hanyar gida filin wasa da babu kamar sa a duniya. Barcelona na kan gagarimin shiri da sabon sauyi. Atletico Madrid ta gina sabon filin wasa, wanda a cikin sa za a buga wasan karshe a Champions League a Madrid.
Juventus fa? Ita ma sabon filin wasa. PSG da Liverpool na gagarimin sauyi. Manchester City na sabon filin wasa. Arsenal da Tottenham sun yi sabon filin wasa.
Mancchester United fa? Babu sabon filin wasa, babu sabbin ’yan wasa, babu kwararrun ’yan wasa, kuma an ki gyara tsohon filin su na kaka da kakanni, wato Old Traffpord.
Ana ganin idan har dan Sarkin Saudiyya, Yarima Salman, wanda ke shugabancin kasar a yanzu ya amince ya sayi kungiyar daga hannun ’ya’yan Glazer, to za ta iya dawowa cikin hayyacin ta nan da shekaru kadan.
Amma dai hakikanin gaskiya shekaru 14 da Man U ta yi a hannun Glazers, Turawan kasar Amurka, ci gaba ta rika samu, amma na mai ginar rijiya.