Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Jami’a, JAMB, ta tabbatar wa wadanda suka rubuta jarabawar shiga jami’a ta 2019, cewa za ta fito da sakamakon jarabawar shiga jami’a a ranar 29 Ga Afrilu.
Jam’in Hulda da Jama’a na JAMB, Fabian Benjamin ne ya bayyana haka a wata hira da aka yi da shi yau Asabar a Bwari, hedikwatar JAMB.
Ya ce ba da dadewa ba za a kammala yi wa sakamakon binciken kwakwaf, yadda za a sake shi jibi Litinin kowa ya na abin da ya samu.
Dalili kenan ya ce a fara sauraren fitowar sakamakon daga ranar Litinin.
Da ya ke magana a kan bin diddigin sakamakon JAMB da za a yi daga jarabwar 2009 zuwa 2019 kuwa, Benjamin ya ce ba za a fara ba tukunna sai bayan an fito da sakamakon 2019 cikin mako mai zuwa.
Ya ce JAMB ta dauko wannan gagarimin shiri ne domin a dakile satar jarabawa tare da kama masu satar jarabawar.
Hukumar ta ci gaba da cewa za ta saki sakamakon 2019 bayan kammala bincike, yadda za ta kama wadanda suka yi satar jarabawa.
Tsarin zai zakulo wadanda suka yi rajista sau biyu, tare da wadanda suka yi rajistar bai daya a wata makarantar ‘ya’yan manya, wadanda a karshe suke baddala bayanan sunayen masu rubuta jarabawa.
Ya ce kamata ya yi sakamako ya fito cikin kwana daya zuwa awa 48 bayan kammala jarabawa. Amma saboda ana so a wannan shekara a tantance tsakanin tsaki da tsakuwa abin zai kai cikin mako mai zuwa. Ba kamar a shakarar 2017 da 2018 ba.
Discussion about this post