Hukumar Ladabtar da Masu Aikata Rashawa (ICPC), ta yunkura domin kwace wasu kadarori mallakar Gidauniyar Shehu Musa Yar’Adua Foundation.
Hakan ya biyo bayan zargin Gidauniyar da aka yi da laifin karya ka’idojin mallakar filaye ko kadarori da ke cikin dokokin kasar nan.
Wata sanarwa da Kakakin ICPC, Rasheedat Okoduwa ta sa wa hannu, ta ce za ta kwace kadarorin ba da dadewa ba.
Ta ce kwacewar da za a yi wa kadarorin na wucin-gadi ne, sannan daga bisani kuma ICPC za ta garzaya kotu domin a ba ta iznin karbe kadarorin dindindin.
Shehu ‘Yar’Adua shi ne yayan tsohon Shugaban Kasa, Umaru ‘Yar’Adua, wanda ya rasu cikin watan Mayu, 2010.
ICPC ta ce kadarorin da za ta kwace sun a a wurare daban-daban ne a Abuja, kuma kudin su sun kai jimillar naira biliyan 4.8.
ICPC ta ce kadarorin wasu kamfanoni 30 ne suka mallake su.
Daga cikin kadarorin da za kwace, akwai wata eka 22.9 ta wani filin da ba a yi gini a cikin sa ba. kuma akwai wani gida, akwai Plaza da wata katafariyar gona ta Maidubu Farm and Construction Limited da sauran su.
ICPC ta ce za ta kwace kadarorin ne biyo bayan korafin da Hukumar Tara Kudaden Haraji ta Kasa, FIRS ta kai cewa an ki biya wa kadarorin haraji har kusan naira milyan 288.2
Discussion about this post