TIRKASHI: Kotu ta dakatar da hukumar Zabe daga ci gaba da tattara zaben Bauchi

0

Kotu a garin Abuja ta dakatar da hukumar zabe daga ci gaba da tattara sakamakon zaben Karamar hukumar Tafawa Balewa da take yi a yau.

A hukuncin da mai shari’a Inyang Ekwo ya karanto ya bayyana cewa dole hukumar zabe ta dakatar da wannan tattara zabe bisa sabawa wasu dokokin shari’a da hukumar ta saba.

Gwamnan jihar Bauchi Mohammed Abubakar tare da jam’iyyar sa ta APC sun maka hukumar Zabe a kotu bisa kokarin bayyana sakamakon zaben Bauchi a karo ta biyu bayan wanda aka bayyana a baya.

Idan ba a manta Gwamnan Jihar Bauchi, Mohammed Abubakar ya bayyana cewa zai yi amfani da duk wata dama da dokar kasa ta ba shi domin ya maka Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) kara a kotu.

Abubakar ya ce bai yarda da hukuncin da INEC ta yanke daga cewa za ta sake tattaro sakamakon zaben Karamar Hukumar Tafawa Balewa har ta yi amfani da kididdigar da ta yi wa gyara ba.

Gwamnan ya na ja-in-ja da INEC ne a zaben gwamna da aka gudanar na ranar 9 Ga Maris, wanda aka samu tankiya a sakamakon zaben Tafawa Balewa.

Bayan an kammala hada sakamakon kowace karamar hukuma, Babban Jami’in Zabe na INEC na Jihar Bauchi, Farfesa Mohammed Kyari ya bayyana cewa zaben bai kammalu ba.

Sai dai kuma Kakakin Yada Labarai na INEC, Festus Okoye, ya ce INEC ta tura kwamitin bincike a Jihar Bauchi, wanda ya tantance inda aka yi aringizon kuri’un da a farko aka ce an soke kuma ya ji ba’asin ainihin abin da ya faru da sakamakon zaben Karamar Hukumar Tafawa Balewa.

Bayan da kwamiti ya je, INEC ta ce za a ci gaba da tattara sakamakon, saboda akwai kwafen takardar sakamakon, wadda kowa ya shaida cewa ita ba ta salwanta ba.

Kotu ta ce a dukkan su su bayyana a kotu ranar 20 ga watan Maris domin ci gaba da sauraren shari’ar.

Share.

game da Author