Tsohon Kakakin tsohon gwamnan jihar Kaduna Ramalan Yero, Ahmed Maiyaki ya tattara nasa-inasa ya fice daga Jam’iyyar PDP zuwa Jam’iyyar APC.
A sanarwar da ya fitar ranar Asabar a garin Kaduna, Maiyaki ya ce babban dalilin da ya sa ya fice daga PDP shine don rashin gamsuwar sa da zabin Isah Ashiru a matsayin Dan takarar gwamnan Jihar Kaduna.
” Idan za ka yi wa kanka adalci ba da irin dan takarar da PDP ta tsayar bane za a musanya goga irin El-Rufai a Kaduna. Nasir El-Rufai ya yi abin azo a gani da irin su Ashiru ba za su iya tabuka komai ba. A dalilin haka kuwa na ga ya fi dacewa mu mara wa El-Rufai baya domin ci gaban Jihar mu.
” Na dade in tattaunawa da neman shawara kafin na yanke wannan shawara. Babu wani dantakara a Kaduna da zai iya kwatanta irin ayyukan da El-Rufai yake yi a Jihar, wannan kowa ya gani Kuma ya shaida.
Maiyaki Wanda shine kakakin gwamnatin Kaduna a lokacin mulkin Ramalan Yero, ya mara wa Sani Sidi baya ne a Zaben fidda gwani na Jam’iyyar.
Akwai yiwuwar Sani Sidi da wasu daga cikin ‘yan Jam’iyyar PDP zasu biyo Maiyaki zuba Jam’iyyar APC din nan ba da dadewa ba.
Wani jigo a Jam’iyyar PDP a Kaduna, Umar Mohammed ya bayyana wa wakiliyar mu cewa sam ba su yi mamakin ficewar Maiyaki daga PDP ba.
” Dama can mun san da cewa zai Koma APC tun ba yanzu ba. Dama can yana tare da tsohon gwamna Ramalan Yero ne, amma ya juya Masa baya a Zaben fidda gwani na PDP ya koma yana yi wa Sani Sidi aiki. Bayan Ashiru ya naka su duka da kasa sai suka fara neman ficewa. Abinda nake so A sani shine itama APC zai fice idan yaji ba dadi.” Inji Umar.