Masu garkuwa sun halaka mutane shida a Sabon Sara, jihar Kaduna

0

An tabbatar da kashe mutane shida da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba, suka yi a kauyen Sabon Sara, kusa da Kidandan, Karamar Hukumar Giwa, Jihar Kaduna.

Bincike ya nuna cewa mahara sun dira cikin garin da karfe 1:30 na dare, a ranar Asabar ta jiya, inda suka yi kokarin sata tare da yin garkuwa da wani mai suna Alhaji Nasidi.
Nasidi dai shahararren manomi ne a kauyen Sabon Sara.

Wani ganau da aka yi dauki ba dadi a kan idon sa, ya bayyana cewa dandazon mahara sun shiga kauyen, inda suka yi kokarin yin garkuwa da Alhaji Nasidi, amma ba su dace ba, sai suka dauki matar sa suka yi kokarin gudu da ita.

Majiyar ta ce su kuma matasa da majiya karfin kauyukan wajen sai suka yi gangami suka bi maharani aka yi kare-jini-biri-jini, har suka kwato matar Alhaji Nasidi daga hannun masu masu garkuwa da mutanen.

“To a wurin kwato ta ne mahara suka bude wuta, suka kashe mutane shida, wasu takwas kuma suka ji raunuka.

“Cikin wadanda suka hakarci rufe gawarwakin na su har da Shugaban Karamar Hukumar Giwa, Injiniya Abubakar Shehu Lawal Giwa da kuma Sakataren Karamar Hukumar Giwa, Alhaji Usman Ismail.”

Sauran wadanda aka ji wa ciwo kuma an garzaya da su asbitin Kauran Wali, da ke Gaskiya, a Zaria.

Share.

game da Author