SABON HARI: Mahara sun bindige mutane 29 a Zamfara

0

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Zamfara ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa mahara sun kashe mutane 29, a wani sabon hari da suka kai shekaranjiya Alhamis.

Kakakin rundunar mai suna Muhammad Shehu, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa wadanda aka bindige har lahira su 29, an tare su ne a lokacin da suke cikin jerin gwanon motoci, kan hanyar su ta komawa gida kware, bayan sun gama cin kasuwar Shinkafi, da ke cikin Karamar Hukumar Shinkafi.

Ya ce mahara sun yi musu kwanton bauna ne a ranar Alhamis, 28 Ga Fabrairu.

Ya ce a cikin dare bayan sun samu kiran gaggawa, an hada rundunar jami’an tsaro da suka hada da ‘yan sanda da sojoji, suka garzaya inda aka yi kisan.

Ya ce sun samu gawarwaki 13 a wurin, sauran 16 kuma a can wani wuri daban suka same su.

Wadannan 16 kamar yadda kakakin jami’an tsaron ya shaida wa wakilin mu, ya ce duk gawarwakin na ‘yan kato-da-gora ne wadanda mahara suka kashe.

Wannan ne mummunan hari da mahara suka kai a Zamfara tun bayan kammala zaben shugaban kasa a ranar 23 Ga Fabrairu.

Tun bayan sake zaben Buhari, har yau bai yi wani kakkausan kalami dangane da mummunan rikicin kashe jama’a a cikin kauyuka da yawaitar sace mutane da ake yi a Zamfara ba.

Share.

game da Author