Akalla mutane 18 ke rasuwa a duk awa daya a Najeriya a dalilin kamuwa da Tarin Fuka – Kwararru

0

Wasu kwararru daga cibiyar hana yaduwar cutar tarin fuka na Najeriya sun koka kan yadda cutar ke kisan mutane a kasar nan.

Shugaban cibiyar Lovett Lawson ta bayyana cewa akalla mutane 18 ke rasuwa duk awa daya a dalilin kamuwa da cutar.

Lawson ta fadi haka ne a wata zama da cibiyar ta yi domin daukan matakan da ya kamata wajen wayar da kan mutane game da cutar a ranar cutar tarin fuka ta duniya.

An kebe ranar 24 ga watan Maris domin wayar da kan mutane game da cutar domin dakile hanyoyin yaduwar ta.

Lawson ta ce abin takaici ne yadda duk kokarin da ake yi wajen hana yaduwar cutar amma har yanzu cutar na kara yaduwa inda a yanzu haka Najeriya na jerin kasashen Afrika da cutar ta yi wa katutu.

Ta ce rashin samun kula ga mutanen dake dauke da cutar, rashin zuwa asibiti domin yin gwajin cutar na daga cikin matsalolin da ake fama da su.

” Bincike ya nuna cewa mutum daya dake dauke da cutar na iya harba wa mutane 15 zuwa 20 wannan cutar idan ba a nemi magani ba ko kuma kulan da ya kamata cikin gaggawa.

A dalilin haka Lawson ke kira ga mutane da su rika zuwa asibiti domin yin gwajin wannan cutar. Sannan a hanzarta zuwa asibiti a duk lokacin da mutum ke tarin da ya kai wata uku.

A karshe ta kuma yi kira ga gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari kan kara ware kudade da daukan matakan da za su taimaka wajen hana yaduwar cutar a kasar nan.

Share.

game da Author