Mahara sun bindige DPO da wasu ‘yan sandan uku a jihar Edo

0

Wasu mahara dauke da bindigogi sun kai wa ofishin ‘yan sandan dake kauyen Afuze a karamar hukumar Owan jihar Edo hari inda suka bindige DPO da wasu ma’aikatan ofishin guda uku.

Kakakin rundunar ‘yan sanda Chidi Nwabuzor ya sanar da haka ga wakilin PREMIUM TIMES ranar Laraba inda ya ce maharan sun aikata wannan ta’asa ne da karfe takwas na daren Talata.

Nwabuzor ya ce maharan su 10 da suka dirar wa ofishin sun bindige DPO ‘yan sandan, wani sifeto da wasu mata biyu inda a cikinsu akwai mai cikin wata bakwai.

” Maharan sun kuma jefa wa ofishin ‘yan sandan bam sannan suka kona wasu motocin ‘yan sandan kuma.

Bayan nan Nwabuzor ya ce maharan sun kai wa ofishin hukumar zabe dake yankin hari itama.

Ya ce rundunar ‘yan sanda na yin bincike domin kamo wadanda suka aiakata wannan mummunar aiki.

A karshe gwamnan jihar Godwin Obaseki ya yi juyayin abin da ya faru sannan ya yi wa iyalen ‘yan sandan da aka kashe ta’aziyya.

Share.

game da Author