Wani likita kuma farfesa a jami’ar Alex Ekwueme dake Ndufu-Alike jihar Ebonyi Chukwunonso Ejike ya gano wata sabon maganin kawar da cutar siga wato ‘Diabetes’.
Ejike ya fadi haka ne a taron inganta aiyukkan fasaha da kera-kere da aka yi a Enugu.
Ya ce ya gano maganin ne mai suna ‘Vog Tea’ bayan shekaru hudu yana gudanar da bincike akai.
” Na yi shekaru hudu ina bincike kan wannan magani. Ina ta gudanar da gwaji kan wannan ganye da da na gano.”
Ejike ya ce hukumomin tattance ingancin magunguna na kasa ta kusa kammala tattance ingancin maganin sannan yana sa ran cewa da zarar sun kammala, maganin zai shiga kasuwa.
Idan ba a manta ba a kwanakin baya ne wasu likitoci daga kasar Amurka suka yi kira ga mutane musamman maza da su yi kokarin ganin basu kamu da cutar ‘Diabetes’ cewa cutar na rage karfin azzakarin namiji.
Likitocin sun gano haka ne a binciken da suka gudanar a kan mutane miliyan 30 a kasar Amurka.
Sakamakon da binciken da wadannan likitoci suka yi ya nuna cewa mai dauke da cutar na tattare da matsalolin cututtukan dake kama zuciya da cututtukan dake kama huhu wanda hakan kadai na iya rage karfin gaban namiji.
Bincike ya nuna cewa cutar siga na kama mutum ne idan aka samu matsala da wasu daga cikin ababen da ke sarrafa abincin da muke ci a cikin mu.
” Shi Insulin ya na aiki ne a jiki wajen tace sinadarin ‘Carbonhydrate’ dake cikin abincin da muke ci don samar wa mutum kuzarin da yake bukata a jiki. ”
A dalilin rashin aikin ‘Insulin’ yadda ya kamata ne ya ke sa a kamu da cutar siga.