Majalisar Dattawa ta tafi hutu sai bayan zaben shugaban Kasa

0

Majalisar dattawa ta tafi hutu sai bayan an kammala zaben shugaban kasa.

A zaman majalisar ranar Alhamis, mataimakin shugaban ta Ike Ekweremadu ya bayyana wa sanatocin da suka halarci zaman majalisar cewa yau ne ranar karshe da majalisaer za ta zauna har sai bayan an kammala zaben shugaban kasa a watan Faburairu.

Kafin majalisar ta dage zaman ta, sai da aka karanta kudirin kankantar albashi da fadar shugaban kasa ta mika wa majalisar.

Ekweremadu ya bayyana cewa gaba kudirin dake gaban su, kudiri ce da ke nuna gwamnati ta amince da naira 27,000 a matsayin sabon karancin albashin ma’aikaci a akasar nan da ya hada da jihohi.

Daga nan sai majalisar ta mika kudirin ga kwamitin ta domin ci gaba da aiki a akai zuwa ta dawo daga hutu.

Share.

game da Author