Malaman kwalejin koyar da aikin malunta sun janye yajin aiki

0

Shugaban Kungiyar malaman Kwalejin koyar da aikin Malunta (COEAS) Nuhu Ogirima ya bayyana cewa kungiyar ta janye yajin aikin da ta fara a watanni biyu da suka gabata.

Ogirima ya sanar da haka ne wa manema labarai a Abuja da suka kammala zaman tattauna matsalolin su da gwamnati.

Ya ce COEASU ta amince ta dakatar da yajin aikin ne bisa ga tabbacin biyan manyan bukatunsu da gwamnati ta yi a wannan zama da suka yi.

Sai dai Ogirma ya ce idan har gwamnati ta ki cika alkawurran da ta dauka za su koma yajin aikin su.

Ogirima ya kuma bayyana cewa gwamnati ta amince ta dawo da ma’aikatan da ta kora a kwalejin da ke dake Ogun.

Idan ba a manta ba (COEASU) ta fara yajin aiki ne a ranar 9 ga watan Oktoba a dalilin rashin biyan bukatun su da gwamnati ta ki yi.

Wadannan bukatu kuwa sun hada da rashin biyan albashi, rashin ingantattun kayan aiki da gini da sauran su.

Share.

game da Author