‘Yan sandan jihar Ogun sun cafke wani magidanci mai suna Shina Kasali mai shekaru 38 da laifin kashe matar sa Sofiat Kasali da dukan tsiya.
Kakakin rundunar Abimbola Oyeyemi ya sanar da haka wa manema labarai ranar Talata inda ya bayyana cewa Kasali ya aikata wannan ta’asa ne a gidan su dake Agbado, karamar hukumar Ifo ranar daya ga watan Disamba.
Oyeyemi ya ce rundunar ta sami labarin ta’asar da Kasali ya aikata ne bayan karar da wani makwabcin sa mai suna Tunde Babatunde ya kawo ofishin su.
” Sofiat ta gamu da ajalinta ne bayan zallar duka da ta sha daga dukan mijinta kawai don ya nemi ta je ta debo masa ruwan da dare ita kuma taki. Ko da muka shigo gidan sai muka same ta a kwance sharaf. Ta dai rasu ne tun kafin mu kai fa isa asibiti.
A bayanan da aka fitar daga ofishin ‘yan sandan, ita Sofiat ta dade tana gurza wa mijin ta rashin mutunci, tun bayan da ya rasa aikin sa. Ba ta yi masa biyayya ko da na kwabo ne. A wannan dare dai da shi mijin cika sai ya kasa hakuri ya hauta da duka har sai da ya ga bata motsi.
Oyeyemi yace Kasali na tsare a ofishin su har sai an kammal bincike akai tukunna.