Wasu mahara dauke da manyan bindigogi sun kashe malamin Kwalejin Fasaha ta jihar Osun, kuma suka arce da libai biyu da ma’aikatan kwalejin su shida.
Wanda aka kashe din mai suna Olaniyi Emmanuel, ma’aikaci ne a bangaren tattara bayanan daliban kwalejin.
Amma kuwa ya zuwa yau da safe, PREMIUM TIMES ta gano cewa dabiban biyu da aka tsare da su, sun kubuta, kuma su na a hannun jami’an ‘yan sanda.
Jami’in yada labaran kwalejin mai suna Adewale Oyekanmi, ya ce an kai musu harin ne da yammaci a lokacin da ake tashi daga aiki.
Ya kuma bayyana dukkanin sunayen wadanda aka arce da su din.
Oyekanmi ya kara da cewa mahara sun datse titin Esa-Oke, hanyar da ta dangana zuwa kwalejin fasahar, suka rika tsayar da motoci. Ta haka ne suka saci ma’aikata da daliban suka arce da su.
Shugaban Kungiyar Daliban Kwalejin mai suna Adekunle Adeleke, ya zanta da PREMIUM TIMES, kuma ya ce daliban da suka tsere daga masu garkuwar, sun ce masa Fulani ne.
Sun yi garkuwar da misalin karfe 4:30 na yammacin Talata.
Kakakin yada labarai na ‘yan sandan jihar ya tabbatar da faruwar garkuwar, kuma ya ce jami’an sun a kokarin ceto sauran mutane shida da ke tsare a hannnun maharan.