Gwamnati ta gyara cibiyoyin kiwon lafiya 4,000 a kasar nan – Faisal Shu’aib

0

Shugbana hukumar kula da kiwon lafiya a matakin farko Faisal Shu’aib ya bayyana cewa Gwamnati ta gyara cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko 4,000 daga cikin 10,000 din da ta yi alkawarin gyarawa a kasar nan.

Idan ba a manta ba shekaru biyu da suka gabata ne gwamnatin tarayya da na jihohi da kungiyoyin bada tallafi suka hada hannu domin ganin an gyara cibiyoyin kiwon lafiya akalla 10,000 a kasar nan.

Sai dai kuma bincike da muka yi ya nuna cewa ba a tabuka komai ba a kai kusan ma rufa-rufa aka yi.

Cibiyar ‘Civil Society Legislative Advocacy Centre (CISLAC)’ ta bayyana cewa cibiyoyin kiwon lafiyar dake kasar nan sun kai 30,000 inda kashi 20 bisa 100 ne daga cikin su ke aiki yadda ya kamata.

A yanzu dai mace daya cikin mata 13 ke mutuwa a duk lokacin da za su haihu saboda mata sun gwammace su ga ungozoma maimakon su tafi asibitoci domin gani kwararrun likitoci.

Share.

game da Author