Buhari ya dai na jingina gazawar sa ga gwamnati na – Goodluck Jonathan

0

Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya daina jingina gazawar sa ga mulkin sa.

Jonathan ya bayyana cewa gazawar da Buhari ya yi ne ya sa a kullum aka tambaye shi bisa dalilan da ya sa aka samu akasi a mulkin sa sai ya jingina hakan ga gwamnatin sa da ta shude.

Idan ba a manta ba Kakakin shugaban kasa Garba Shehu ya bayyana a hira da gidan talabijin na Channels cewa matsalolin da ka samu a tafiyar wannan gwamnati sun hada da tabargazar da gwamnatin Jonathan ta tafka a lokacin da take mulkin kasar nan.

Da aka tambayi Garba ko menene dalilin da ya sa gwamnatin Buhari ta dade bata nada ministoci ba wanda wasu ke ganin hakan na da nasaba da abin da yasa aka samu matsaloli a gwamnatin Buhari ya ce Jonathan ne ya yi sanadiyyar hakan cewa bai mika wa Buhari takardun musaya na ayyukan gwamnati ba sai awa 48 kafin a rantsar da shi.

A martani da Jonathan ya fitar, ya ce a sanin sa dai irin wadannan takardu ba su kunshe da sunayen ministoci da kullum aka yi magana sai ace shine dalili.

Share.

game da Author