Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta fatattaki mai horas da ‘yan wasan kungiyar Jose Mourinho.
Hakan ya biyo bayan rashin tabuka abin azo a gani ne da mai horas da ‘yan wasan yayi a tsawon shekarun sa yana aiki a kolub din.
Yau dai ya cika shekara 3 da kwana daya cif kenan da korar sa da kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta yi bayan ya kaza tabuka komai a Kolub din.
Mahukuntar kungiyar sun sanar cewa za ta sanar da sabon mai horas da ‘yan wasa zuwa karshen wannan zangon wasa.