Shugaba Muhammadu Buhari ya koka da yadda Kungiyar Jinkai Ta Duniya, wato ‘Amnesty International’ ke nuna bangaranci da kuma rashin adalci a rahotannin da ta ke fitarwa dangane da Najeriya da kuma yaki da Boko Haram.
Cikin makon da ya gabata ne sojojin Najeriya suka bada sanarwar korar kungiyar daga ayyukan jinkai da ta ke yi a yankin da ake yaki da Boko Haram.
Sai dai kuma kwana daya bayan korar, aka janye batun inda fadar shugaban kasa ta fito ta ce bangarorin biyu za su yi zaman sasanta gano inda matsalar ta ke.
Kwana biyu bayan nan kuma sai sojoji suka kara jaddada cewa lallai ba su bukatar Amnesty International a yankin Arewa maso Gabas.
Jiya Litinin kuma, kakakin yada labarai na Buhari, Malam Garba Shehu, ya bayyana damuwar gwamnati a kan irin rahotannin son zuciya da gwamnatin ta Buhari ta yi zargin Amnesty International na fitarwa.
Sanarwar da Garba ya fitar daga fadar Shugaban Kasa ta nuna cewa duk da gwamnatin Buhari ta yarda kuma ta na bada hadin kai kan dalilan kafa kungiyar Amnesty, amma gwamnatin ta hakkake cewa kungiyar na kawo mata cikar wajen yaki da Boko Haram, musamman wajen karya guyawun sojojin Najeriya daga irin rahotannin da ta ke fitarwa.
Buhari ya ce gwamnati na ganin kamar ma ta na yaki biyu ne a lokaci guda. Na farko yaki da Boko Haram, na biyu kuma yaki da Amnesty International.
Daga karshe ya roki kungiyar da ta yi duba da binciken ayyukan jami’an ta a Najeriya, musammaan a kan batun da ya shafi yaki da ta’addanci.