Masu garkuwa sun sako matar Sarkin Adara, sun rike sarkin

0

Masu garkuwa da mutane sun sako matar Sarkin Adara da ke cikin Karamar Hukumar Kachia, Jihar Kaduna.

An sako ta ne ranar Lahadi da safe, kuma kamar yadda rundunar ‘yan sandan Kaduna ta sanar, matar na a hannun likitoci su na duba lafiyar ta asibitin garin Kachia.

Sai dai kuma har yanzu ba su saki mijin Victoria din ba, wato basaraken na Adara mai suna Maiwada Galadima.

Kakakin ‘yan sandan na Kaduna ya ce ana bakin kokarin ganin an saki sarkin tare da direban sa mai suna Timothy da aka kama su aka yi garkuwa da su tare.

Kamfanin Dillancin Labarai ya ce an kashe mutane hudu, ciki har da dan sanda daya kafin a gudu da basaraken da matar sa da kuma direban na sa.

Share.

game da Author