WATA SABUWA: Dan takarar gwamnan Kwara na PDP bai je NYSC ba, satifiket na jabu ya mallaka

0

Dan takarar gwamnan jihar Kwara a karkashin jam’iyyar PDP, Razak Atunwa, bai je aikin yi wa kasa hidima na NYSC ba, kamar yadda dokar kasa ta tanadar tilas.

PREMIUM TIMES ta gano cewa da bai je ba, sai ya damka wa jam’iyyar PDP satifiket na sahale masa zuwa aikin, amma na jabu, kamar yadda tsohuwar Ministar Harkokin Kudade, Kemi Adeosun ta yi.

PREMIUM Times ta tabbatar da cewa da wannan satifiket ne jam’iyyar PDP ta tantance Atunwa.

Wannan badakala ta fito ne watanni hudu bayan PREMIUM TIMES ta bankado irin ta da Kemi Adeosun ta yi.

Sannan kuma PREMIUM TIMES ta bankado wannan dan takarar gwamna a jihar Kwara ne, wata daya daidai bayan ta bankado cewa shi ma Ministan Sadarwa Adebayo Shittu bai je aikin bautar kasa ba.

Da wannan rahoo ne jam’iyyar APC ta ki tantance Shittu daga neman fitowa takarar gwamna da ya yi na jihar Oyo, a karkashin jam’iyyar APC.

Dokar Najeriya dai ta shar’anta cewa duk wanda ya kammala jami’a, matsawar dai bai cika shekaru 30 kafin kammalawar ta sa ba, tilas sai ya yi aikin yi wa kasa hidima na tsawon shekara daya, wato NYSC kafin ya fara aiki a wani wuri tukunna.

An haifi Atunwa dan takarar gwamnan jihar Kwara a ranar 17 Ga Oktoba, 1969, ya karanci aikin shari’a a Jami’ar London, inda ya kammala cikin 1992 a lokacin ya na da shekara 23.

Tunda Atunwa ya kammala digirin sa na farko a lokacin da ya ke shekaru 23 bayan haihuwa, dokar NYSC ta Sashe na 2 ta wajibta masa tafiya aikin NYSC na shekara daya kenan.

KARFIN HALIN MALLAKAR SATIFIKET NA JABU

Maimakon Atunwa ya tafi aikin bautar kasa, sai ya yi zaman sa a Ingila, bai dawo ba sai cikin 2005, inda ya na dawowa aka nada shi mukamin kwamishina a karkashin Bukola Saraki a lokacin da ya ke gwamnan jihar Kwara.

Lokacin da Atunwa ya zama kwamishina, har ya kai shekaru 36 da haihuwa.
Ttsakanin 2005 zuwa 2010, Atunwa ya yi kwamishina har sau hudu, ciki kuwa har da kwamishinan Kasa, Ayyuka, Sufuri, Yada Labarai da na Kudade.

Sai dai ba a sani ba ko Atunwa ya mika wa hukuma wata shaida ta NYSC a lokacin da ya yi kwamishina da kuma cikin 2011 da ya zama Kakakin Majalisar Jihar Kwara da kuma 2015 da ya zama dan majalisar tarayya.

Amma kuma ya samu zama dan takarar PDP na gwamnan jihar Kwara a ranar 1 Ga Oktoba, 2018, bayan ya damka wa jam’iyyar PDP satifiket na jabu. Hakan kuwa na nuni da cewa ya kantara kaya kenan, laifin da zai iya janyo masa daurin shekaru 14.

Idan ba a manta ba, bayan PREMIUM TIMES a fallasa Minista Kemi Adeosun, ta yi murabus, washegari kuma ta gudu zuwa Landan.

Ko ya gwamnatin Buhari za ta yi da Kemi, Shittu da Atunwa?

Share.

game da Author